Kwalara ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyar a Legas

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Rahotanni daga Jihar Legas na cewa a ƙalla kimanin mutane biyar ne suka mutu yayin da aka garzaya da mutum sittin asibiti sakamakon ɓullar cutar kwalara a yankunan Eti Osa, Lagos Island, Ikorodu da kuma Kosofe.

Kwamishinan ma’aikatar lafiya na Jihar, Farfesa Akin Abayomi ya fadi a lokacin fitar da wani rahoto na musamman kan aukuwar lamarin inda ya ce gwamnatin jihar ta samar da hanyoyin hana cigaba da yaɗuwar cutar.

Akin ya kuma bayyana cikin alhini cewa wadanda suka mutu an same su ne cikin mutanen da aka kai su asibiti a ƙurarren lokaci.

Bugu-da-ƙari, ya ce ma’aikatar lafiya da hukumomin kula muhalin Jihar na gudanar da bincike kan gurɓacewar ruwa a yankin wanda hakan ke sababba yaɗuwar cutar da ma wasu a faɗin Jihar.

By Babaji