
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yayin da ake bikin cikar demokradiyya shekaru 25 a Najeriya, shugaba Bola Ahmed Tinubu yayi faɗuwar ba zata a lokacin da yake ƙoƙarin hawa matakalar motar zagaye a filin taro na ‘Eagle Square’ dake Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa, babu wani rauni ko ɗimuwa da Tinubu ya samu a lokacin aukuwar lamarin inda nan-da-nan aka ga ya cigaba da jawabi kan al’amurran da suka shafi taron da sauran abubuwa.
A wani rubutu da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai a kafafan sada zumunta, Dada Olusegun yayi, an samu ƙarin haske kan batun inda ya ce shugaba Tinubu ya faɗi ne sakamakon kuskuren taka matakala da yayi gabanin fara taron inda aka ga ba abun da ya same shi na rauni, domin an cigaba da gudanar da taron kamar yadda aka tsara.
Ƙari a kan haka, aukuwar irin lamarin ba shi ne farau ba, domin kuwa makamancin haka ya faru ga shugaban ƙasar Amurka Joe Biden a shekarar 2021 yayin da yake ƙoƙarin hawa matakalar shiga jirginsa mai tashin Angulu.
