Shugaba Tinubu Mutum ne kamar kowa: Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai na musamman, Bayo Onanuga ya kare shugaba Tinubu biyo bayan tuntuɓe da ya yi a filin taron ‘Eagle Square’ dake Abuja a ranar Laraba.

A yau ne demokradiyyar Najeriya ke cika shekaru 25 inda shugaba Tinubu ya haɗu da jarabawar faɗuwa gabannin fara jawabinsa a filin taron

Bayo, ya ce faruwar hakan kan auku da kowa kuma a kowane lokaci inda ya bada misali da Biden da Obama na Amurka waɗanda irin haka ya sha faruwa da su, dan haka lamarin bai da tasiri wajen gudanar da ayyukan gwamnatinsa.

Sannan, wannan lamari bai sa Tinubu ya samu rauni ko kuma haifar da cikas wajen gudanar da jawabinsa da kuma ayyukan da aka tsara a taron ba.

By Babaji