Gwamnatin Tinubu ta amsa tana biyan tallafin fetur

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bayan kwashe tsawon watanni ana musantawa, a ƙarshe Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta amince da cewa ƙasar da ta fi kowacce ƙasa haqo mai a nahiyar Afirka za ta ware har naira tiriliyan 5.4 domin tallafin man fetur a shekarar 2024.
Wannan adadi ya qaru sosai daga Naira tiriliyan 3.6 da aka kashe a shekarar 2023 da kuma Naira tiriliyan 2.0 a shekarar 2022.
An bayyana hakan ne a lokacin da Wala Edun, ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin ƙasa ya gabatar da wani shiri na inganta zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa (ASAP), wanda aka tsara don tunkarar manyan ƙalubalen da suka shafi ayyukan yin garambawul da kuma bunƙasa cigaba a ɓangarori daban-daban na tattalin arziki.
“A halin yanzu, ana hasashen kashe kuɗaɗen tallafin mai da zai kai tiriliyan N5.4 a ƙarshen shekarar 2024. Wannan ya kwatanta rashin dacewa da tiriliyan N3.6 a 2023 da tiriliyan N2.0 a 2022,” inji daftarin kwafin ASAP da Edun ya gabatar.
A baya dai gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ba za ta sake bayar da tallafin fetur ba, a maimakon haka ta zaɓi tsarin da ya dace.
A watan Disamba, gwamnatin ta ce saɓanin ikirarin da bankin duniya ya yi na cewa gwamnati na ci gaba da biyan tallafin man fetur, zamanin tallafin man fetur ya “ƙare”.
A wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels TV, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai a Nijeriya, Mohammed Idris ya ce shugaba Tinubu ya bayyana ƙarara tun daga ranar farko da ya hau mulki cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.
Ministan ya ce, cire tallafin ya canja zuwa ƙarin kuɗaɗen shiga da ke tarawa a asusun tarayya.

By ukarofi