Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, inda ya bayyana cewa a shirye yake ya tattauna da wakilan gwamnati.
Kanu ya bayyana hakan ne a cigaba da shari’ar da mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ke jagoranta.
Shugaban ƙungiyar ta IPOB ɗin dai yana hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) tun a shekarar 2021 inda aka sake kama shi tare da dawo da shi domin ci gaba da shari’ar sa bisa zarginsa da laifin ta’addanci da cin amanar ƙasa.
Sai dai a zaman da aka cigaba da sauraron ƙarar a ranar Laraba, babban lauyan sa, Mista Ejimakor Aloy, ya shaida wa kotun cewa har yanzu hukumar leƙen asirin ba ta cika umarnin kotun ba, yana mai cewa har yanzu an hana su kai Kanu ziyara, inda ya ce sashe na 17 na dokar babbar kotun tarayya ya bayar da damar cimma masalaha ta tattaunawa.
Jagoran lauyoyin Nnamdi Kanu, Alloy Ejimakor, ya shaida wa kotu cewa sun nemi amfani da sashe na 17 na dokar babbar kotun tarayya ne domin fargabar za ta soke buƙatunsu guda biyu.
Buƙatarsu ta farko ita ce kotu ta garƙame shugaban DSS, Yusuf Bichi bisa zargin karya umarnin kotu.
Sai buƙatarsu ta biyu ta tuhumar kotun da cewa ba ta da hurumin sauraron shari’ar, kuma tuni lauyan gwamnati Adegboyega Awomolo ya yi martani.
Ya ce babban karewa ya fara tattaunawa da wanda ake ƙara kan tuhumar da ake masa.
“Na ce masa ya je wurin Babban Lauyan Tarayya (AGF) wanda ke da iko. Idan yana sha’awar tattaunawa, to ya je can, ofishinsa yana nan,” inji Awomolo.
Mai shari’ar a martanin da ta mayar ta ce: “Kotu ba ta da matsala da ita idan ɓangarorin na son a tattauna a kan batun, amma Kanu ya tunkari AGF wanda ya dace ya tattauna da shi.”
lauyan ƙasa ne kawai yake da ikon tattunawa kan zarge-zargen da su ka shafi cin amanar ƙasa da ta’addanci.
A cikin muhawarar da ya yi, Awomolo ya shaida wa kotun cewa ba shi da umarnin wanda ya ke
