Gwamnatin Tinubu za ta sayo wa Fadar Shugaban Ƙasa sabon jirgi bayan gwanjon tsofaffin jirage uku

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar sayar da tsofaffin jiragen sama na ofishin shugaban ƙasa domin sayo sabo wa ofishin.

Hakan ya faru ne bayan da kwamitin majalisar wakilai kan tsaron ƙasa da basira ya bada shawarar cewa akwai buƙatar a sayo jirage guda biyu domin amfanin shugaban ƙasa da na mataimakinsa.

Shugaban kwamitin na ɓangaren majalisar dattijai, Shehu Buba Umar ya bada goyon bayansa kan shawarar majalisar wakilan.

Rahoton ya ƙara da cewa, sayar da jiragen zai taimaka wajen samun daidaito kan adadin da ake buƙata a ofishin, domin yanzu haka akwai jirage gama gari guda shida da kuma masu ƙirar helkofta guda huɗu wanda hakan ya zama jimillar guda 10.

A halin yanzu, gwamnatin ta naɗa wani masanin harkokin jiragen sama ɗan ƙasar Amurka a matsayin wanda zai jagoranci sayar da su inda a yanzu haka an sanya yarjejeniya tsakaninta da shi tare da ƙoƙarin sayan jirgi mai tashin angulu yayin cinikin.

By Babaji