An kama ɗan shekara 20 da satar yara a Legas

Spread the love

An samu wata hatsaniya a yankin Ojurowo da ke bangaren Eko jihar Legas. Wata mata a ka kama da sata da sayar da ƙananan yara.

Jaridar City Round ta rawaito cewa, matar ta saci yaran daga Ijora sannan ta kawo su Eko don ta sayar.

A wani faifan video dake yawo a shafin sada zumunta na X, an ga mutane zagaye da wani gini da ake zargin nan wannan matar ke aiwatar da haramtaccen kasuwancin ta.

Kamar yadda aka jiyo sautin wani a faifan bidiyon, yana cewa matar ta amsa cewa za ta siyar dasu a kan kuɗi naira 250,000. Ke nan ko wanne yaro zai kama ta siyar dashi kan naira 50,000.

Duk da wannan, mai magana da yawun ‘ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin a wata hira da akayi dashi, yace an kama wani matashi mai suna Maxwell Nweke mai shekaru 20 da satar yara biyar a tsibirin Legas.

By ukarofi