An sace motar ’yan sanda ta ofishinsu da ke Abuja

Spread the love

MAHDI M. MUHAMMAD

An samu rahoton sace wata farar mota ƙirar Toyota Hiluɗ Pickup mai lamba FG79-A23, mallakar rundunar ’yan sanda ta tarayya a Abuja. Lamarin ya faru ne a unguwar Gwarimpa a daren ranar Talata.

Motar da aka sace wata kadara ce ta Gwamnatin Nijeriya kuma ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ce ke amfani da ita. 

Wannan ma’aikatar ita ce ke da alhakin ƙaddamarwa, tsarawa, da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka shafi ‘yan sanda da tsaro na cikin gida.

Har ila yau, tana bada kulawa da tallafi na gudanarwa ga rundunar ‘yan sanda ta Nujeriya (NPF), makarantar horar da ‘yan sanda (POLAC), da sabuwar asusun kula da ‘yan sandan Nijeriya (NPTF).

Har yanzu dai ba a fayyace cikakkun bayanai game da satar ba, amma hukumomi na gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin. 

An sanar da jami’an tsaro, kuma ana cigaba da ƙoƙarin kwato motar da aka sace. 

Ma’aikatar ta buƙaci jama’a da su bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen gano motar da kuma kamo masu laifin.

Wannan satar dai na nuni da irin ƙalubalen tsaro da ake fama da shi a babban birnin ƙasar tare da jaddada buƙatar inganta matakan kare kadarorin gwamnati da tabbatar da tsaron lafiyar al’umma. 

Ma’aikatar harkokin ‘yan sanda ta jaddada ƙudirinta na inganta ƙa’idojin tsaro don hana afkuwar irin haka nan gaba.

Za a samar da ƙarin bayanai yayin da bincike ke cigaba. Ana kira ga jama’a da su kasance cikin taka tsantsan tare da kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

By ukarofi