Majalisar Jihar Sokoto ta amince da dokar rage wa Sarkin Musulmi ƙarfi bayan da ƙudurin ya wuce karatu na ɗaya da na biyu.
Ƙudurin in har ya zama doka, zai ragema sarkin Musulmi ƙarfin iko musamman wajen naɗin dagatai.
Wannan na zuwa ne bayan da ƙungiyar MURIC ta yi shelar cewa gwamnan na son tuɓe Sarkin Musulmin, wanda gwamnatin jihar ta ƙaryata.
