Nijeriya za ta nemi gudunmawar rigakafin Kwalara bayan ta’azzarar annobar cutar

Spread the love

Gwamnatin tarayya na tunanin neman rigakafin cutar kwalera ganin yadda annobar cutar ke ƙara ta’azzara a ƙasar.

Shugabar hukumar Gavi, Dr Sania ta wallafa a shafinta na X cewa, Gavi ta damu da ɓarkewar annobar kwalera a Najeriya, don haka a shirye suke don su bada nasu tallafin rigakafi wajen ganin an shawo kan matsalar.

Magunguna uku da Hukumar lafiya ta duniya ta sahale amfani dasu sun haɗa da Dukoral, Shancol da Euvichol.

By ukarofi