Tsaro: Za mu bar mambobin da aka dakatar su halarci ganawarmu – ECOWAS

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Ƙungiyar Ƙasashen Yankin Afrika Ta Yamma (ECOWAS) ta bayyana cewa, za ta bar mambobin da aka dakatar da cikinta su halarci ganawar da suke yi kan tabbatar da samar da haɗin gwiwar tsaro a yankin.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ministan Tsaro na Nijeriya, Badaru Abubakar, a zaman sauraron ba’asin sakamakon bin diddigin ƙasashen da ƙungiyar ta dakatar a watannin baya saboda juyin mulkin soja a ƙasashen nasu ranar Alhamis a Abuja.

Badaru ya ƙara da cewa, ECOWAS ta na buƙatar aƙalla Dala Biliyan 2.6 a kowacce shekara ga sojojin tsaron haɗin gwiwa a yanki, kamar yadda rahoton binciken kwamitin bin ba’asin ya gano.

A kwanakin baya ne ECOWAS ta tura jakadu zuwa ƙasashe Nijar, Burkino Faso da Mali, waɗanda aka dakatar da su sakamakon samun juyin mulkin sojoji a ƙasashen a bara, amma duk da an yafe mu su tare da dawo da su cikin ƙungiyar, sai suka bayyana ficewa daga cikin ƙungiyar kuma suka kafa tasu ƙungiyar.

A jiya Alhamis ne aka zauna, don jin ba’asin tsaro kan aikin da aka bai wa kwamirin, inda Minista Badaru ya ƙara da cewa, akwai hanyoyin biyu da za a iya amfani da su wajen maganta matsalolin tsaron, waɗanda suka haɗa da samar da isassun sojoji guda 5,000, don magance ta’addanci a yanki, inda hakan zai lamushe aƙalla Dala Biliyan 2.6 duk shekara, ko kuma samar da mafi ƙaranci sojoji guda 1,500, wanda zai lamushe Dala Miliyan 481 a kowacce shekara.

Sai dai ya ce, dukkan waɗannan matakai ba za su yi nasarar da aka fi buƙata ba har sai da haɗin kan kowa. Don haka ne ƙungiyar ta amince da shigar dakatattun mambobin a zaman da za a riƙa yi na samar da dakarun.

“Kowacce mamba ta ƙungiyar a na so ta biya kasanta,” inji Abubakar, “dominn mun yi zuzzurfan nazari kan ƙalubalen tsaron da ke addabar yankin da matsalolin kuɗin da mambobin ke fama da shi wajen yin karo-karonsu.”

Shi ma Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Tourey, ya ƙara jaddada cewa, hatta sauran mambobin da aka dakatar ba za a hana su zaman ganawar ba, ya na mai cewa, “an yi imanin cewa ba za mu iya yaƙi da ta’addanci mu kaɗai ba matuƙar sauran ba su shiga ciki ba.

“Duk da ya ke wasu mambobin ƙungiyar an dakatar da su, amma za a bar su su shigo cikin tattaunawar da ta shafi tsaro. Don haka ne mu ka gayyaci dukkan mambobin guda 15, don halartar zaman ganawar.”

Idan za a iya tunawa, a watan Janairu ƙasashen Nijar, Burkino Faso da Mali sun gayyaci Ƙasar Rasha kan haɗin kan tsaro bayan da suka fatattaki ƙasashen Yammacin Turai, musamman Amurka da Faransa.

Yanzu abinda ya rage a gani shine, irin rawar da waɗanda ƙasashe masu mulkin soja a yankin za su taka a yiwuwar haɗakar.

By ukarofi