Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, wanda har yanzu bai kai ga gurfana a gaban kotu a Abuja ba, ya buƙaci kotun ta mayar da shari’arsa zuwa Jihar Kogi.
Tawagar lauyoyinsa ta ce, Babbar Kotun Jihar Kogi ce kaɗai ke da hurumin shari’a kan zargin da ake yi masa.
Lauyan Bello, Adeola Adedipe, ya sanar da kotun game da wasiƙar da ya aike wa babban alƙalin babban kotun tarayya na neman a miƙa shi ga kotun Kogi.
Mai gabatar da ƙara ya bayyana cewa wannan buƙatar ba ta zama uzurin rashin halartar Bello kotu ba, sannan ya buƙaci kotun da ta yi magana kan halin da ake ciki.
A cigaba da zaman da aka yi a ranar Alhamis, Bello bai gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ba domin cigana da shari’a. Amma lauyansa, Mista Adeola Adedipe, SAN, ya sanar da mai shari’a Emeka Nwite game da wasiƙar da aka aika wa babban alƙalin.
Da yake jawabi a kotun, Adedipe ya ce, “Mai Shari’a, bayan kwana na ƙarshe da aka ɗage zaman, na kai rahoto ga tawagarmu, kuma aka sanar da ni cewa an rubuta wa mai shari’a wasiƙa a madadin wanda ake ƙara zuwa ga mai girma alƙalin babbar kotun tarayya na neman miƙa shari’ar zuwa sashin shari’a na Lokoja, wanda muke ganin yana da hurumin da ya dace.”
An karɓi wannan wasiƙa, kuma ofishin babban alƙalin ya sanar da tawagar masu gabatar da ƙara da su ba da amsa kafin ranar 13 ga watan Yuni, har zuwa safiyar yau (Alhamis), ban samu wani martani daga masu gabatar da ƙara ba, ko kuma wani hukunci kan wannan buƙatar da babban alƙali ya yi.”
Hukumar EFCC, wanda Kemi Pinhero, SAN, ya wakilta, ya buƙaci kotun da ta umarci a yi mata bayanin rashin zuwan Bello kotu, inda ya yi nuni da wani shiri da aka yi a ranar 13 ga watan Yuni domin tabbatar da zuwansa.
Pinhero ya yi watsi da bayanin lauyan da ke kare Bello a matsayin dabarar jinkiri, kuma ya buƙaci kotun da ta ɗauki nauyin manyan lauyoyin da laifin cin mutunci.
Bello, wanda ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas, ana tuhumarsa laifin zagon ƙasa, da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati kusan Naira biliyan 80.2. Ana tuhumar sa tare da ɗan uwansa Ali Bello da wasu mutane biyu, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu da hannu wajen karkatar da kuɗaɗe.
Duk da a baya bai gurfana a gaban kotu ba, ƙungiyar lauyoyin Bello ta shigar da buƙatar a ajiye sammacin kamo shi da aka bayar a ranar 17 ga Afrilu tare da ƙalubalantar hurumin kotun. Bello ya yi ikirarin cewa hukumar EFCC ta bijirewa hukuncin da wata babbar kotun jihar Kogi ta yanke a lokacin da ta shigar da ƙara a gabanta tare da neman a kama shi.
Ko da yake kotun ta ƙi bayar da umarnin kama shi a ranar 10 ga watan Mayu, amma ta bai wa Bello damar gabatar da kansa bisa raɗin kansa domin gurfanar da shi.
