
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli, Antonio Conte ya ce ya amince da buƙatar Victor Osimhen na son barin ƙungiyar a kakar wasan bana.
Conte ya faɗi hakan ne kasancewar akwai yarjejeniya tsakanin ɗan wasan Nijeriyan da kuma Napoli.
Ƙwararren ɗan jaridan wasannin, Fabrizio Romano ya ruwaito cewa, Conte ya ce yana sane da yarjejeniyar da ke tsakanin ɗan wasan da kulob ɗin saɓanin sauran ƴan wasa.
Ganin haka ke da wuya, ake ta jita-jitar cewa Conte na son kawo ɗan wasan ƙasar Baljika, Rumelu Lukaku domin maye gurbin Osimhen.
