Tinubu da wasu manyan ƙasashe sun taya Starmer murnar lashe zaɓen Birtaniya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da wasu shugabannin ƙasashe sun taya Sir Keir Starmer na jam’iyyar Labour murna, biyo bayan nasarar da ya samu a babban zaɓen da aka gudanar a ƙasar Birtaniya.

Nasarar da Starmer ya samu, ta sa zai zama sabon firaministan ƙasar bayan da Rishi Sunak ya shafe shekaru 14 a kan kujerar.

Tuni dai Rishi ya amince da faɗuwa a zaɓen bayan shan kaye da ya yi da rinjaye mai yawa.

A lokacin da ya ke jawabi cikin wata sanarwa, mai taimaka wa shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya ce, a matsayinsa na tsohon shugaban jam’iyyar adawa a Nijeriya, Tinubu ya bayyana cewa zimma da jajircewa sun taimaka wa Starmer wajen yin nasara a zaɓen.

Sanarwar ta ce Tinubu ya kuma taya ƴan ƙasar da gwamnatinsu murna ganin yadda demokradiyya ke samun martabawa daga gare su wanda hakan ya mayar da tsarin shugabancinsu nasu abin kwaikwayo ga sauran ƙasashe.

Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa, Nijeriya za ta ƙarfafa alaƙarta da Birtaniya musamman a ɓangarorin da za su taimaka wajen kawo cigaba da kuma ɗabbaka harkokin demokraɗiyya.

By Babaji