Sama da Indiyawa 100 sun mutu a wurin bikin addini

Spread the love

Hukumomin Indiya sun tabbatar da mutuwar mutane 116 sakamakon turmutsitsi a yayin wani dandazon taron addini a wannan Talatar.

Mutanen sun rasa rayukansu bayan halatar taron addini na ƙabilar Hindu a Hathras da ke arewacin ƙasar, kuma galibinsu mata ne da ƙananan yara.

Wata mai suna Shakuntala da ta ganewa idonta yadda lamarin ya faru ta ce duk jama’ar wurin sun fara tserewa ne bayan kammala taron addinin.

Wani babban jami’in ɗan sanda, Shalbh Mathur ya ce adadin mutanen da suka je taron sun haura yawan waɗanda aka ba wa izinin zuwa.

Babban Ministan jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath, wanda mabiyi addinin Hindi ne ya miƙa saƙon jaje tare da umarnin ƙaddamar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin.

A Ƙasar Indiya, an saba da ganin afkuwar ibtila’i a yayin tarukan addini inda ko a shekarar 2013 mutum 115 ne suka mutu a wani taron da aka yi a kusa da gadar Madhaya Pradesh a 2018 inda mutum 224 suka mutu sama da 400 suka jikkata a yankin Jodhpur da ke Arewacin Indiya.

By ukarofi