Za a kara tsakanin Massoud Pezeshkian da Saïd Jalili a zaɓen shugabancin Iran

Spread the love

A Ƙasar Iran kasancewa a zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa na 2024, wata ɗaya bayan mutuwar shugaba Ibrahim Raïssi, zagayen farko ya bayar da dama na zaɓen magajin Raissi ba, sai an je zagaye na biyu tsakanin ɗan takarar neman sauyi Massoud Pezeshkian wanda ya samu kashi 40% da ɗan takarar masu ra’ayin riƙau Saïd Jalili ya zo a matsayi na biyu da kashi 38.5% na ƙuri’un.

Bincike ya bayyana cewa kashi 60% na Iraniyawa sun ƙi fitowa rumfunan zaɓe, alamar rashin gamsuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma murƙushe masu zanga-zangar da suka biyo bayan mutuwar Mahsa Amini a watan Satumban 2022.

Zaɓen na bana dai na cikin zaɓuɓɓuka mafiya tsauri da ke samun sanya idanu daga ƙasashen turawa ƙwarai da gaske, la’akari da halin da ƙasar ke ciki da kuma yanayin mu’amalarta da ƙasashen duniya a diflomasiyyance.

By ukarofi