Hukumar tace fina finai za ta sanya ƙafar wando ɗaya da masu zanen ƙwarangwal a jikin Adaidaita

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

A yau ne, hukumar tace fina finai da ɗabi’a ta Jihar kano ta bada sanarwar cewa za ta sanya ƙafar wando ɗaya da masu zane dake yiwa matuƙa baburan adaidaita zanen banza.

Wannan na fitowa a wata sanarwa daga jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, inda yace Shugaban hukumar Abba Elmustapha ya ɗau wannan alwashi ne a lokacin da ƙungiyar masu sana’ar zane suka kai mashi ziyara ƙarkashin jagorancin Malam Muhammad Kabir. Ya ƙara da cewa, duk wani mai zane da yake da hannu wajen yin zane na cin mutunci, ko ɓata tarbiya da duk wani nau’in zane na cin zarafi zai fuskanci fushin hukumar.

Jagoran ƙungiyar ya bayyana cewa a shirye suke su ba hukumar goyon baya domin cimma wannan buri nata.

Daga ƙarshe jagorancin Ƙungiyar sun yaba wa shugaban hukumar saboda yadda aka mutunta su domin ganin suma su samu cigaba

By ukarofi