
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yayinda shahararren ɗan ƙwallon ƙafan duniya Christiano Ronaldo da takwaransa na ƙasar Portugal, Pepe ke shirin bankwana da buga wasa, ƴan wasan sun yi rashin nasara a hannun Faransa a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar kofin Nahiyar Turai na 2024.
Portugal ta sha kaye ne a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida bayan shafe mintuna 120 ba a samu wanda ya zura ƙwallo ba, inda daga baya Faransa ta doke ta da ci 5 da 3.
Wannan ita ce gasar kofin ƙasashe ta ƙarshe da ƴan wasan biyu su ka sha alwashin ajiye aikinsu da ƙasar daga kan ta kasancewar sun shafe sama da shekaru ashirin ana fafatawa da da su a mataki na ƙasa da kuma na ƙungiyoyi inda su ka samu nasarori da dama ciki har da nasarorin zaman zakaran ɗan ƙwallon duniya sau 5 da Ronaldo ya yi.
Sai dai, wasan ƙarshen da su ka buga, bai wa magoya bayansu daɗi ba kasancewar sun yi fatan nasara a gare su, amma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.
