Arsenal ta ɗauki zaɓin sayen mai tsaron gidanta Daɓid Raya da tauka aro daga Brentford kan kuɗi fan miliyan 27.
Raya mai shekara 28 ya buga wasannin gasar firimiya 16 ba tare da an zura masa ƙwallo a raga ba.
An zura masa ƙwallo 16 ne kacal a gasar firimiya sannan a ƙarshe ya lashe kyautar maitsaron ragar da ya fi kowanne ƙoƙari a kakar da ta gabata.
Arsenal tana da mai tsaron ragarta Aaron Ramsadale, wanda ya buga mata wasanni 38 na kakar da aka yi ta 2022/23, ya buga wasanni 14 ba tare da an zura masa ƙwallo ba, kuma hakan ya sanya Mikel Arteta ya samu nutsuwa a zaɓin masu tsaron ragarsa.
A watan Agusta, ɗan wasan Sifaniya ya sanya hannu kan kwataragin shekara biyu da Bees kafin daga bisani ya koma Gunners a kakar a matsayin aro mai tsayi.
Barcelona na ƙoƙarin sayen ɗan wasan gaba na ƙasar Sifaniya Dani Olmo daga RB Leipzig, inda kungiyar ta ƙasar Sifaniya ke ƙoƙarin amincewa da shirin biyan kuɗin ɗan wasan mai shekaru 26 da haihuwa kan Yuro miliyan 60.
Ɗan wasan gefe na Brazil Willian ya ƙi amincewa da tayin sabon kwantiragi a Fulham, inda ƙungiyoyi a Saudiyya da Turkiyya ke zawarcinsa.
Ɗan wasan tsakiya na Paris St-Germain Ethan Mbappe, ɗan uwan kyaftin din Faransa Kylian, na shirin ƙulla yarjejeniya ta dogon lokaci a Lille, ɗan wasan mai shekaru 17 bai taba tattaunawa da Real Madrid ba saboda ɗan ƙasar Faransa yana son cigaba da zama a Ligue 1.
Everton na sha’awar ɗauko ɗan wasan Kamaru Jackson Tchatchoua, mai shekara 22, yayin da Hellas Ɓerona ta Italiya ke son ɗan wasan bayan kan kusan Euro miliyan 8.
Atalanta na shirin ɗauko ɗan wasan tsakiya na Italiya Nicolo Zaniolo a matsayin aro daga ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya.
Barcelona za ta yi niyyar sayar da ɗan wasan baya na Uruguay Ronald Araujo da ɗan wasan Brazil Raphinha a bazarar nan domin ɗauko ɗan wasan gaba na Athletic Bilbao da Spain Nico Williams, mai shekara 21, zuwa Camp Nou.
Chelsea na zawarcin ɗan wasan baya na Nottingham Forest Murillo amma suna ganin farashin ɗan ƙasar Brazil din mai shekaru 21 da haihuwa ya yi tsada sosai.
Ana hasashen ɗan wasan bayan AC Milan Theo Hernandez zai kammala komawa Manchester City kan fan miliyan 51, inda a halin yanzu ɗan wasan mai shekaru 26 ke taka leda a Faransa a gasar Euro 2024.
Ɗan wasan tsakiya na Chelsea Conor Gallagher zai yi “jinkirin” komawa Aston Ɓilla yayin da ɗan Ingilan mai shekaru 24 ke jiran sabuwar yarjejeniya da Blues.
An yi watsi da tayin da Arsenal ta yi na Yuro miliyan 47 kan ɗan wasan baya Riccardo Calafiori daga Bologna, inda ake neman aƙalla yuro miliyan 50 kan ɗan wasan na Italiya. Chelsea ma zawarcin ɗan wasan mai shekaru 22.
Manchester United za ta tattauna kan neman da ƙungiyoyi ke yi wa kyaftin ɗinta Bruno Fernandes, mai shekara 29, amma ana sa ran ɗan wasan tsakiyar na Portugal zai cigaba da zama a ƙungiyar tare da sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya.
An hango Dele Alli yana atisaye tuƙuru yayin da yake ƙoƙarin neman sabon kulob bayan barin Everton lokacin da kwantiraginsa ya kare a ƙarshen kakar wasan da ta gabata.
Ɗan wasan bayan Faransa William Saliba zai iya barin Arsenal a bazara, inda Real Madrid ke zawarcin ɗan wasan mai shekaru 23.
Ana sa ran ɗan wasan Napoli Ɓictor Osimhen, mai shekara 25, zai buga wasannin share fage a mako mai zuwa, a daidai lokacin da Manchester United da Chelsea da kuma Arsenal ke zawarcin ɗan wasan na Nijeriya.
West Ham na tunanin maka sabon tayi kan ɗan wasan bayan Nice Jean-Clair Todibo bayan ta yi watsi da tayin fan miliyan 24.5 kan ɗan wasan na Faransa mai shekaru 24.
