Wannan ne Euro na ta ƙarshe – Ronaldo

Spread the love

Kyaftin ɗin Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa gasar Euro 2024 ce za ta zama Euro ɗinsa ta ƙarshe.

Ronaldo ya bayyana hakan ne bayan da Portugal ta fitar da Sloɓenia a bugun fenariti a wasan da suka fafata a zagaye na 16 a daren Litinin.

Ɗan wasan mai shekaru 39 ya ɓarar da bugun fenariti, to sai dai tsohon ɗan ƙwallon Manchester United da Real Madrida Juɓentus ya sharɓi kuka.

Sai dai Ronaldo ya zura ƙwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, yayin da Diogo Costa ya yi bugun daga kai sai mai tsaron gida.

“Tabbas wannan zai zama Euro na ta ƙarshe,” inji Ronaldo ga manema labarai.

“Amma wannan bai girgiza ni ba. Hankali ya kwance yake.

Portugal ta kai daf da na kusa da na ƙarshe, bayan da ta yi nasara a kan Sloɓenia da cin 3-0 a bugun fenariti ranar Litinin a Euro 2024.

Tun farko tawagogin sun tashi ba ci a minti na 90 da suka fafata, daga nan aka ƙara musu minti 30, nan ma ba a fitar da gwani ba.

Mai tsaron ragar Portugal, Diego Costa ne ya tare ƙwallo ukun da ta haɗa da ta Josip Ilicic da Jure Balkoɓec da kuma ta Benjamin Ɓerbic

An kuma bai wa kociyan Sloɓenia, Matjaz Kek jan kati a wasan a karin lokaci.

Da wannan sakamakon Portugal, za ta fuskanci Faransa a zagayen daf da na kusa da na karshe ranar Juma’a.

Faransa ta kai gurbin kwata fainal, bayan da ta ci Belgium 1-0 ranar Litinin.

Wannan shi ne karo na biyu da suka fafata a tsakaninsu, inda Slovenia ta doke Portugal 2-0 a wasan sada zumunta a watan Maris a Ljubljana.

Har yanzu Sloɓenia ba ta taɓa cin wasa ba a gasar kofin nahiyar Turai ta Euro a tarihi.

A Euro 2000 ta yi ban kwana a zagayen cikin rukuni da maki biyu, wadda a bana ta yi canjaras uku ta kare a mataki na uku.

Wasa ɗaya Sloɓenia ta taɓa yin nasara a babbar gasar tamaula, shi ne 1-0 da ta ci Algeria a gasar cin kofin duniya a 2010.

Sloɓenia ɗaya ce daga ƙungiyoyin da suka yi canjaras uku a karawar cikin rukuni a tarihin gasar cin kofin nahiyar Turai.

Portugal ta taɓa yin haka a Euro 2016, wadda ta kare a mataki na uku da maki uku, amma ta kai ga lashe kofin,

Haka itama Denmark canjaras uku ta yi a bana a Euro 2024 kamar yadda Slovenia ta yi a Jamus.

By ukarofi