Za a karrama fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil Pele a ƙasarsa tare da ƙaddamar da bikin “Ranar Sarki Pele”, inji jaridar gwamnatin ƙasar a ranar Talata.
Kasancewarsa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa a tarihi, Edson Arantes do Nascimento – wanda aka fi sani da Pele – ya lashe gasar kofin duniya sau uku tare da Brazil kuma ya zura ƙwallaye sama da 1,000 a tarihin rayuwarsa.
Za a gudanar da “Ranar Sarki Pele” a ranar 19 ga Nuwamba – ranar da ɗan wasan ya ci ƙwallonsa ta 1,000 a wasan da kulob ɗinsa ta Santos ta doka a filin wasa na Maracana na Rio de Janeiro a shekarar 1969.
Ƙwallon da Pele ya ci ya fito ne daga bugun fenariti a wasan da suka doke Ɓasco da Gama da ci 2-1, kuma an katse wasan na ɗan lokaci yayin da magoya bayansa suka mamaye filin domin murnar nasarar Pele.
Ɗan asalin Tres Coracoes ya sadaukar da nasarara cin ƙwallon ga ‘ya’yan matalauta na Brazil.
A shekara ta gaba, ya lashe gasar kofin duniya na ƙarshe a gasar kofin duniya guda uku a matsayin wani ɓangare na nasararar Brazil a 1970.
Pele ya mutu ne a ranar 29 ga Disamba, 2022, yana da shekaru 82. Rasuwar tasa ta doki zuciyar al’umma daga sassan duniya.
Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva ne ya ƙaddamar da dokar samar da ranar tunawa da Pele.
