A Inter Miami zan ajiye ƙwallo – Messi

Spread the love

Shahararren ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi ya yanke shawarar rataye takalmansa daga ƙwallon ƙafa a Inter Miami. 

Ɗan wasan mai shekara 36, mai kyautar Ballon d’Or takwas, ya koma buga gasar ƙwallon ƙafa ta Amurka a kakar wasa ta 2022/23, bayan da kwantiraginsa ya ƙare a Paris St-Germain.

Kyaftin ɗin na tawagar Argentina ya nuna kansa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, inda ya lashe gasar Kofin Zakarun Turai sau huɗu da La Liga 10 a ƙungiyar da ke Sifaniya. Wanda ya ɗauki kofin duniya a 2022 da Argentina a Katar a 2022, yana da sauran ƙunshin yarjejeniya da za ta kare a Inter Miami zuwa ƙarshen kakar wasa ta shekarar 2025.

Kawo yanzu dai ɗan wasa Messi yana wasa kan ganiya ba za ka ce zai yi ritaya kwanan nan ba, wanda ya ci ƙwallo 12 da bayar da 13 aka zura a raga a wasa 12 a gasar ta Amurka.

Kuma kawo yanzu yana wakiltar ƙasar Argentina a gasar kofin kudancin Amurka wato Copa America, da a yanzu ake bugawa a ƙasar Amurka a bana, wadda ita take da kofin da ta ɗauka a 2021 a Brazil.

By ukarofi