Buga ƙwallo da robar kariyar fuska babu daɗi – Mbappe

Spread the love

Ɗan wasan ƙasar Faransa, Kylian Mbappe ya ce ba daɗi buga ƙwallo da robar kariyar fuska, bayan Faransa ta fuskanci Belgium a karawar zagaye na biyu a Euro 2024 ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Mai shekara 25 ya ji rauni a karan hanci a wasan farko a cikin rukuni da Faransa ta ci Austria 1-0 a gasar ta cin kofin nahiyar Turai.

Bai buga wasa na biyu ba da suka tashi ba ci da Netherlands, amma ya kara a fafatawa ta uku a cikin rukuni da suka tashi 1-1 da Poland.

A karawar ce Mbappe ya buga da robar kariyar fuska, wanda ya ce bai samu sukuni ba.

Mbappe ya sanar cewar kafin fuskantar Belgium a Dusseldorf “Yin ƙwallo da abin kariyar fuska ba daɗi.

“Ina ta sauya kariyar fuskar, domin ina cin karo da wani abin da ya kamata a kara ko kuma a cire.

“Gaskiya da wahala, domin yana rage min gani, kuma gumi baya sauka daga goshi, har sai na cire kariyar fuska.

“Amma tunda ina iya cire fuskar kariyar ba wata matsala, kuma bani da wani zaɓi.

“Abin dai ba wani daɗi, amma ina godiya ga kariyar fuskar da ta bani damar buga wasannin.”

By ukarofi