De Zerbi ya karɓi aikin horar da Marseille

Spread the love

Marseille ta sanar da naɗa Roberto de Zerbi a matakin sabon kocinta.

De Zerbi ya bar Brighton bayan kammala kakar da ta wuce, bayan shekara biyu da ya ja ragamar ƙungiyar da ke buga firimiyar Ingila.

Ɗan ƙasar Italiya, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka uku, ya maye gurbin Jean-Louis Gasset, wanda ya yi ritaya, bayan ƙarƙare kakar da ta wuce.

De Zerbi tsohon kocin Shakhtar Donetsk ya karɓi aikin horar da Brighton cikin Satumbar 2022 kan kwantiragin kaka huɗu.

Ya kai ƙungiyar mataki na shida a kakar farko a firimiya – mataki mafi girma da ta taka da samun gurbin buga gasar zakarun Turai a karon farko a tarihin ƙungiyar.

Sai dai Brighton ta karkare a mataki na 11 a kakar da ta kare da kai wa ’yan 16 a Europa League, daga nan ya ƙulla yarjejeniyar ajiye aikin horar da ƙungiyar.

Gasset, tsohon kocin Montpellier da Bordeauɗ ya maye gurbin Gennaro Gattuso a matakin riƙon ƙwarya cikin Fabrairu.

Ya ja ragamar Marseille ta kare a mataki na takwas a teburin Ligue 1, gurbin rashin ƙoƙari tun bayan 2016.

By ukarofi