Muna farin ciki da kulawar da Gwamna Abba ke bayarwa ga bunƙasa Kwalejin Ilimi ta Ghari – Dakta Abdullahi Asiru

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana mataki da Gwamnan  Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ke ɗauka  na farfaɗo da bunƙasar ilimi da har aka dawo da cigaba da  karatu a Kwalejin ilimi ta Ghari da cewa abu ne  na mutuƙar jin daɗi  da farin ciki ga cigaban al’ummar Jihar Kano.

Dakta Abdullahi Asiru shugaban Kwalejin Ilimi ta Ghari ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida  ya ce al’ummar ƙaramar hukumar  Ghari da na Kano ta  Arewa da su  da aka ɗorawa nauyi da amana na  shugabancin Kwalejin da masu kishin Ilimi a Jihar Kano baki ɗaya na murna  da dawo da makarantar duba da yadda a Gwamnatin baya aka yi wa ilimi riƙon sakainar  kashi da ta kai ga rufe ta, yanzu zuwan Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta ɗauki matakai na farfaɗo da inganta ilimi a Jihar Kano ta dawo da makarantar.

Ya ƙara da cewa Kwalejin Ilimi da share fagen shiga jami’a ta Ghari yanzu ana nan ana ayyuka a cikinta sakamakon alƙawari da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi  ana aikin kewaye Kwalejin da katanga  da ƙofofi na zamanil.

Ya ce duk wani taimako da Gwamna ya yi alƙawari na inganta Kwalejin  an fara ayyuka, kama daga kan samar da kujeru na karatun ɗalibai da ƙoƙarin  samar da kayan aiki.Yanzu haka ɗalibai masu karatun NCE na ɗaya da na biyu dana Uku  suna nan suna karatu sannan suna  shiirin ɗaukar sabbin ɗalibai a Kwalejin Wanda yanzu haka akwai ɗalibai 350 suna karatu.

Ya ce a ƙiyasi nan gaba  kaɗan za su ɗebi sabbin ɗalibai sama da  3000 da za suyi kwasa kwasai daban  daban da ake gudanarwa a kwalejin ilimi ta Ghari na neman shaidar NCE da  na share fagen shiga jami’a.

Dakta Abdullahi Asiru ya ce Gwamnatin Jihar Kano ta yi alƙawarin samar da kayan aiki da malamai ga kuma Kwalejin ta tabbatar da ita ,ba abinda ya rage musu  illa su bada gudunmawa wajen bunƙasa ilimi ta tsayawa  suyi aiki tuƙuru a matsayinsu na shugabanin kwalejin don cimma manufar Gwamnati na bunƙasa ilimi da yardar Allah.

Ya ce babban fatansu da burinsu Kwalejin Ilimi ta Ghari ta zama zakaran gwajin dafi a  Kano ta Arewa, saboda babu wata babbar Kwalejin Ilimi kamar ta ,sannan ƙaramar hukumar Ghari na da kusanci da jihohi biyu ta ɓangaren Kazaure tana da kusanci da jihar Jigawa sannan ta na da kusanci da jihar katsina ta ɓangaren gidan mutum ɗaya wanda zai kasance hatta ɗalibai daga jihohin maƙota za su ci gajiyar samun karatu a kwalejin.

Ya ƙara da cewa   Kano ta Arewa tana da aƙalla  ƙananan hukumomi 13  don haka nema a Kwalejin suke  da shiri na  baiwa shugabannin riƙo  na ƙananan hukumomin yankin  takardu na  ɗaukar ɗalibai kyauta  a kwalejin domin su baiwa ɗalibansu da suka cancanta a da za a ɗauka  domin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce musu a taimakawa ɗalibai  su yi karatu, ba an samar da makarantar ne   domin neman riba ba sai don Ilimi .

Shugaban kwalejin Ilimi ta Ghari ya ce makarantar tana da wurin kwanan ɗalibai da filayen wasanni da ɗakunan karatu kuma ɓangaren Mata da na maza daban suna da kuma manyan rijiyoyin burtsatse ba su da matsalar ruwa kuma Gwamnati ta yi musu alƙawarin sanya musu manyan injuna masu zuko hasken rana domin a samarda wuta dan samun cikakken kulawa na koyo da koyarwa.

Sannan a ɓangaren tsaro Kwalejin Ilimi ta Ghari a  kusa take da  ofishin yansandan yankin  har ma shugaban ma’aikata na Gidan Gwamnatin Kano ya haɗa  su da shugaban sojoji harma   hukumar makarantar  ta kai masa ziyara  ya yi  musu alƙawarin taimaka musu ta sanya sojoji wajen kulada   tsaro a  kwalejin  sannan  suna addu’oi na neman kariyar Ubangiji  ga makarantar.

Shugaban kwalejin Ilimi na Ghari ya yi nuni da  cewa kasancewar  Jihar Kano   gari ne na   musulunci  wanda shi ya tsara  tarbiyya kyakkyawa, ɗalibansu masu ladabi da biyayya ne, da kuma  son karatu.Akwai ma shiri da suke so suyi nan gaba na  bada wasu ajujuwa a cikin  kwalejin  da za a mayar wajen karatun islamiyya, wanda Kwamishinan Ilimi mai zurfi Dakta Yusuf Kofar Mata ya sahale ayi hakan dan daɗa bunƙasa cigaban Kwalejin.

Dakta Abdullahi Asiru ya ce Allah shine shaida tunda aka basu amanar shugabancin Kwalejin suke ta  faɗi tashi da ma’aikatansa, akwai mataimakinsa Hamisu Musa Gambo Ɗanzaki da  rijistarar Kwalejin Muktar Shehu Alhayat da mai kulada kuɗaɗenta  Mubarak Abba da kuma babbar mai kulada ɗakin karatu Jamila Mansur Chiranci waɗannan mutane biyar dashi kansa kullum tare suke  tunda aka buɗe Kwalejin 1/1/2024 basa zama aiki suke kodayaushe.

Ya ce Allah shine masani  cikakken burinsu su ga Kwalejin Ilimi ta Ghari ta jera da  duk wata  Kwalejin Ilimi da ke ƙasar nan, koma ta fita saboda yanzu sun zama cikakkiyar kwalejin Ilimi, kwanan nan dokar su zata fito da aka sahale musu zama cikakkun masu bada shaidar NCE burinsa ya ga ɗalibansu suna gogayya da duk wasu  ɗalibai, duk wata shaidar karatu da ake bayarwa a  makarantun ilimi a ƙasarnan ya zama daidai da nasu

Ya tuna  cewa a lokacinda  Kwankwaso yake Gwamnan  Jihar Kano ya kafa makarantar  Karatun  “IJMB, remedial “ake  Gwamnatin baya da tazo  ta rufe ta,  aka daina karatun   sai  zuwan Gwamna Abba Kabir  ya dawo da ita ya buɗe ta aka ƙara mata kima ta zama cikakkiyar kwaleji da suke  “NCE,IJMB, Remedial” Nan gaba ma  in Allah ya yarda tunda da rarrafe ake tashi har digiri ma sai an yi a kwalejin Ilimi ta Ghari.

Dakta Abdullahi Asiru shugaban kwalejin Ilimi ta Ghari ya ce hatta a ɓangaren bunƙasar tattalin arziƙi makarantar ta Ghari ta bunƙasa Kasuwanci da sufuri da sayar da kayayyakin abinci a garin,  hatta gidajen haya zasu bunƙasa  ta nan ma an taimaki ƙaramar hukumar wajen  ƙarin samun kuɗin shiga da bunƙasar  tattalin arziƙi yan  garin ma  da suke zuwa cirani zasu ragu zasu tsaya suyi sana’oi  a garin hatta Mata zasu sami sana’oi ,dama waje ne na noma.A  kwasa- kwasai  da za suyi akwai na harkar noma da koyon sana’oi da za a riƙa koyawa ɗalibai.

By ukarofi