Ɗan sandan da ya ƙi karɓar cin hancin miliyan N150 ya samu kyautar fili a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ƙarshen makon da ya gabata ne wani Sufetan ‘yan sanda (SP), Ibrahim Ezekiel Sini, wanda ya ƙi karɓar cin hancin Naira Miliyan 150 daga hannun wani ɗan kasuwa a Legas kuma wanda ya kafa Platform Capital, Akintoye Akindele, an karrama shi tare da ba shi fili a Abuja.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, wanda ya ba da kyautar filin a madadin abokan aikinsa na ‘yan sandan, ya ce halin da SP Sini ya nuna ya sa rundunar ’yan sandan Nijeriya alfahari.

Har ila yau, ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya taron, Prince Chukwuemeka Okoye, shugaban kamfanin Ɓegas Homes, ya ce halin SP Sini ya kasance abin koyi kuma ya kamata ya zaburar da sauran jama’ai da ‘yan Nijeriya, domin kuwa hakan ya nuna cewa rundunar ’yan sandan Nijeriya tana da mutane masu gaskiya da riƙon amana.

A cewarsa, “Ayyukan da SP Sini ya yi ba wai kawai ya kawo wa kansa da kuma rundunar ‘yan sandan Nijeriya kwarin gwiwa ba ne, amma ya kuma ƙara ƙarfafa gwiwar wasu da dama da su tsaya tsayin daka wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma bin ƙa’idojin ɗa’a. Amincinsa ta kasance wata fitila, yana nuna cewa ko da a cikin yanayi mai wuya, mutum zai iya kasance da aminci da ƙima.

“Wannan karramawar an yi niyya ne ba kawai don nuna godiya ga kyawawan halayen Sufeto Ibrahim Sini ba, amma don nuna cewa al’umma na yaba wa ɗaiɗaikun mutane masu gaskiya da halin kirki.

“Muna so mu nuna cewa rundunar ‘yan sandan Nujeriya tana da jami’ai da suka kware, wanda hakan zai saka wa jama’a kwarin gwiwar yin aikin ɗan sanda mai ma’ana kuma su zama abin koyi.”

Yayin da yake yaba wa halin Sini, Okoye ya ce taron na ɗaya daga cikin sauran hanyoyin nuna godiya da suke da shi don halayensa na kirki.

“Ƙin amincewa da Naira miliyan 150, tsoron Allah da ƙwarewa. Duk waɗannan halayen jami’in Ibrahim ya nuna,” inji shi.

Idan dai za a iya tunawa, Akindele, wanda wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya ta tsare a gidan yari na Kuje, ana zarginsa da bai wa ‘yan sanda cin hancin Naira miliyan 150 domin samun damar karkatar da binciken da ya ƙaddamar a kansa.

A cewar tuhume-tuhumen, an bayar da cin hancin ne domin ba wa ’yan sanda damar tserewa ƙasar waje da kuma rubuta masa rahoto mai kyau bayan bincike.

An kama Akindele ne a kan takardar koke da Summit Oil International Limited ya miƙa wa shugaban ’yan sandan, kuma an zarge shi da damfarar kamfanin dala 5,636,397 da kuma wani Naira 73,543,764.

A halin da ake ciki, SP Sini ya ce dalilin da ya sa ya ƙi amincewa da kuɗin cin hancin shi ne saboda ya gwammace ya samu natsuwa, ya ci gaba da yin gaskiya a kan aikinsa da kimar rundunar ‘yan sandan Nijeriya da kuma kiyaye mutuncin sunan danginsa.

By ukarofi