Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Shugaban Ƙungiyar nan ta masu motocin sufuri da aka fi sani da NURTW na ƙasa reshen jihar Nasarawa, Alhaji Muhammadu Maiƙwarya, ya ce ba shakka bana musamman a lokutan bukukuwan Sallah da sauran bukukuwa da suka gabata an samu raguwar haɗura sosai a manyan hanyoyin jihar baki ɗaya.
Alhaji Muhammadu Maiƙwarya ya sanar da haka ne a lokacin da yake tattauna da wakilin mu a gidan sa dake birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar a karshen mako daya gabata.
Ya ce tabbas a matsayin sa na shugaban ƙungiyar a jihar akan aika masa da rahotanni da suka shafi adadin hadura akan manyan hanyoyin da sauran su akowannan lokaci a kuma shekara da shekara kuma a rahoton na bana da ya samu dangane da hakan ya gano cewa an samu nasarar raguwar haduran matuka a hanyoyin da suka hade jihar da sauran jihohin ƙasar nan baki daya.
A kan hakan nema yasa shugaban ƙungiyar NURTW din a jihar alhaji Muhammadu Maikwarya yayi amfani da damar inda ya ta’alakanta hakan ga kokarin gwamnatoti a duka matakai musamman na tarayya game da gyara tareda gina sabbin manyan hanyoyin da suke cigaba da yi a hanzu.
A cewarsa tabbas wadannan gyare-gyaren hanyoyin da gine-ginen wasu sabbin suna taimaka nesa ba kusa ba wajen rage haduran wadda yace a da anyi ta samun akasin hakan sakamakon munanan yanayin hanyoyin baki daya. Ya cigaba da bayyana cewa “A gaskiya dole na yi amfani da damar nan don in yaba wa gwamnatotin mu a duka matakai musamman na tarayya dangane da wadannan kyawawan ayukan gyara tareda gina sabbin manyan hanyoyin mu da suke yi a yanzu. A gaskiya hakan yana taimakawa matuƙa wajen rage haɗura a manyan hanyoyin sabanin yadda lamarin yake a da da akayi wasi da batun gyarar hanyoyin, saboda haka dole ne mu yaba wa gwamnati a wannan fannin mu kuma yaba wa direbobi mambobin mu anasu bangaren dangane da bin sabbin dokoki da tsare-tsaren tukin irin na zamani da muke cigaba da horar dasu akansu a kullum,” inji shi.
Alhaji Muhammadu Maiƙwarya ya ƙara da cewa tabbas bayan bin dokokin tuƙin na zamani da sauran su mambobin ƙungiyarsa wato direbobin suna kuma kula da lafiya da kuma dukiyar al’umma yadda yadace ayayin da suke gudanar da sana’ar su na tukin inda yace ba shakka hakan yana nuna ne cewa lallai sunayin amfani da horo da shugabancin ƙungiyar ke yi musu akai-akai yadda ya dace.
Shugaban har ila yau ya kuma yi amfani da damar inda ya yaba wa hukumar kare hadura na ƙasa wato Road Safety a turance dangane da kyakkyawar gudumawa musamman ta hadin kai da ƙungiyar sa ta NURTW da suke yi don tabbatar da rage ko kawo karshen haduran baki daya a manyan hanyoyin jihar dama ƙasa baki daya inda ya bukaci su cigaba da wannan aikin taimako
