Daga MUHAMMADU MAJITTABA a Kano
Gwamni Usman Abdulrahman Dangauro ya bayyana cewa hidimar da Shehu Ibrahim Inyass ya yi wa addini a fannoni daban-daban ya sa suke ƙaunar Shehu Ibrahim Inyass domin a cikin muridansa, ɗalibansa, mahaddata Alkur’ani masu yawa domin da wahala ka samu malami a nan kusa wanda mabiyansa, su ka haddace Alkur’ani kamar Shehu Ibrahim Inyass a wannan lokacin tun daga kan irinsu, Shehu Usman Dahiru Bauchi fitattun malamai, irin su, Gibrima, Malam na Zangon Barebari a nan Kano, irinsu Sheikh Mudi Salga, da dai sauran malamai Arewacin ƙasar nan da Kudanci, har ma da wajen Nijeriya kuma malamai da yawa a Misra da Saudiyya da sauran ƙasashe sun grmama Shehu Ibrahim Inyass saboda baiwa da kuma ilimin da Allah ya ba shi, to wannan ya nuna Shehu iIbrahin Inyass ya yi masa wa addini hidima musamman idan kai la’akari da cewa ‘ya’yansa da jikokinsa mahaddata Alkur’ani ne wannan ba ɓoyayya abu ba ne shi ne babban littafin da musulmin duniya ke alfahari da Imani dashi a matsayin littafi da su ke kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya saukarwa ga Annabinsa S.A.W.
Gwani Usman Abdurrahman Ɗangauro dai masani ne akan tarihin Shehu Ibrahim Inyass a lokacin wani taro, na mabiya ɗariƙar Tijjaniyya da aka gabatar a Unguwar Ɗangwauro Kano a lokacin da ya gabata.
Haka kuma ya ce Shehu wanda kuma Khalifa ne Shehu Ahmadu Tijjani ya yi rubuce-rubuce a fannoni da dama na yabon Annabi kamar littafinsa diwaini haka a fannoni na addini da ya shafi fiƙihu, larabci, nahawu, da dai sauransu, wanda tarihi ba zai taɓa mantawa da tarihi Shehu Ibrahim Inyass a faɗin duniya, waɗanda ba Musulmi ba dubun waɗanda ba Musulmi ba ne su ka shiga musulinci a lokaci guda da kuma lokuta daban daban, dan haka ƙaunarsa da Allah da Manzonsa da kuma biyayya ga Allah da manzo sa, ta sa mu ke ƙaunar shehu Ibrahim Ihyass a cewa gwani usman ɗangauro kano.
Haka kuma Gwani Usman Abdurrahman ya yi karatu a zawuyoyin malaman kano da wajanta ya ce halin da aka shiga a yanzu a Nijeriya akwai buƙatar yawaita tuba ga Allah wato Istigifari, Salatin Annabi, da kuma komawa ga Allah da kuma ɗaukacin Al’umma kowa yaji tsoron Allah ta yadda shugabanni zasu zama masu adalci malamai za suji tsoron Allah ta hanyar faɗar gaskiya komai ɗacin ta domin wa’azi akan faɗar gaskiya shi babban aikin annabawa da sauran bayanin Allah dan haka ya zama wajibi kowa yayi ɗa’a ga Allah maɗaukacin sarki domin amfani duniya da kuma lahira.
A ƙarshe ya shawarci al’umma a kan a haɗa kai domin haɗin kai ne babbar hanyar samun zaman lafiya da ƙaruwar arziƙi a kuma guji, hassada, ƙeta, munafurci, da kuma sauran abun da Allah maɗaukacin sarki ya haramta, a matsayin wata hanya da ke kawo alherin duniya da lahira.
