Daga FAROUK ABBAS
Majalisar Wakilai ta ce tana zargin an yi safarar ‘yan matan da suka ƙaddamar da ƙunar baƙin wake ne a jihar Borno wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama a ranar Asabar da ta gabata.
Wakilin Majalisar, Ahmed Jaha a yayin magana kan wani batu na gaggawa game da al’amarin a Majalisar, ya ce bincike ya nuna cewa an yi hayar ‘yan ƙunar baƙin waken ne daga wajen jihar Borno.
Sannan, aikin tada bom ɗin wanda ya faru a Gwoza, an samu aƙalla mutane sama da 30 ne su ka rasa rayukansu tare da raunata sama da wasu 180.
A lokacin da ya ke jawabi, mai magana da yawun rundunar tsaro na yankin, Manjo Janar Edwerd Buba ya ce aikin, mayar da martani ne ga ‘yan tada ƙayar baya da bai rasa nasaba da nasarar da rundunar soji ke samu a ƙoƙarinta na daƙile ayyukan ‘yan ta’adda a jihar.
An samu tashin bom na farko a wajen wani biki da misalin ƙarfe 3 na rana inda wata ta yi shigar mai bara to zo cikin taron wani biki a titin Mararabar Hausari.
Sai na biyu da ya tashi a titin, bayan wani ɗan lokaci inda ganin haka ya sa rundunar ta sanar da dokar ta ɓaci domin kiyaye aukuwar ƙarin ɓarna a yankin.
Sannan, wani bom ɗin ya sake tashi a karo na uku inda a ka hari jami’an sojin yayinda rasa rayuka uku.
Rundunar ta jajenta wa al’umma tare da kira a gare su da su cigaba da zama masu lura da bada haɗin kai ga jami’an domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a yankunansu.
