Bankin fidelity ya gudanar da ayyuka da yawa na bunƙasa ci gaban al’umma – Isa Inuwa

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Bankin Fidelity ya gudanar da taron ganawa da abokan hulɗarsu da kuma faɗakar da jama’ar Jihar Kano tsarin  sayar da hannun jarin da bankin ya soma.

Daraktan a bankin, Alhaji Isa Muhammad Inuwa ya shaida wa manema labarai a yayin taron da aka yi ranar Talata  cewa sun yi taron ne domin sanar da mutane da jawo hankalin musamman abokan hulɗar su muhimmancin sayen hannun jari a bankin.

Ya ce sun tattauna da nunawa mutane yanda za su iya sayen hannun jarin bankin da kuma dalilai da ya kamata mutane su sanya jarinsu da za a iya sayen hannun jari  daga guda 1000 akan N9,750 kowane ɗaya akan  N9,750  kenan. 

Ya ce bankin na Fidelity ya shigo da hannun jari da za su sayar  a kasuwa guda miliyan 10. Akwai kuma garaɓasa ga waɗanda ke da hannun jarii dama a bankin za su sayar masu hannun jarin akan N9,250 .

Alhaji Isa Inuwa ya ce a tarihin bankin shekaru 30 da kafa shi ba’a taɓa samunsa da wani  laifi ko gazawa ba, sannan ba su taɓa kasa samun riba da suke rabawa ga masu hannun jari ba duk shekara.

Ya yi nuni da cewa da  akwai wani rauni ko  jin tsoro gameda  Bankin na fidelity da  babban Bankin ƙasa CBN ba za su bari  su  sayar da hannun jari ba.

Isa Inuwa ya ce  a yanzu  Bankin na ɗaya daga cikin  waɗanda ke da inganci   a ƙasarnan  suna  mataki na shida a jerin bankuna  masu   nagarta, suna fata nan gaba ma za su zo su taradda sauran waɗanda ke gabansu suma yi musu fintinkau.

Daraktan na Bankin na Fidelity Isa Inuwa  ya ce idan aka zagaya daga Sakkwato zuwa Maiduguri daga Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano za a ga  ayyuka da suke na tallafawa bunƙasa cigaban al’umma a fannoni daban-daban masu yawa kama daga gyaran asibitoci da makarantu da  bada littatafai da kujeru da abinci.

Ya yi nuni da cewa ko a azumin watan Ramadan da ya gabata bankin nasu ya raba dafaffen abinci kyauta kullum lokacin shan ruwa ga mutane 500 a Jihar  Kano.

Alhaji Isa Inuwa ya ce sun kuma gina ɗaki a asibitin masu fama da yoyon fitsari da sanya kayan aiki a ciki da gina sabbin makarantu a Zariya da Maiduguri da Sakkwato da kaduna da cikin kwalejin Rumfa a Kano.

By ukarofi