Gwamnatin tarayya ta sanar cewa a shirye take tsab, domin shigar da Jaridar Daily Trust ƙara saboda rahoton da tayi akan Yarjejeniyar SamoaYarjejeniyar ta buƙaci kasashe dole su kula, da kuma bada kariya ga yan daudu, masu auren jinsi kafin a bada bashin.
Sai dai jaridar daily trust ta rawaito cewa malamai da kuma kungiyoyin sa kai sun yi Allah wadai da wannan al’amari.
Ministan yaɗa labarai ya fito ya maida martani, inda yace Najeriya ta saka hannu ne ga Yarjejeniyar bayan yin watsi da duk wani sashe da yaci karo da al’adu da kuma dokokin Nijeriya.
Ya ƙara da cewa gwamnati na bakin ƙoƙarin ta wajen aiki da ba yan jarida walwalar aiki, amma gwamnati ba zata lamunci labarin ƙarya ba.
Don haka gwamnati ta shirya tsaf don shigar da ƙara domin kare mutuncin ta. Gwamnati ba za ta lamunci wani labari wanda zaiyi barazana ga tsaro da hadin kai na yan ƙasa ba.
