Ɗaruruwan mayaƙan Boko Haram sun tsere daga kurkuku a Jamhuriyar Nijar

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Rahotanni sun bayyana cewa, ɗaruruwan ƴan ta’adda da ɓarayi da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi ne suka tsere daga kurkukun Koutoukale a ƙasar Jamhuriyar Nijar.

Matseretan, sun tsere ne da makamai da kuma ababan hawa bayan da suka gagari jami’an tsaron kurkukun wanda ke kusa da birnin Niamey a ranar Alhamis.

Shaidu sun tabbatar da cewa, an jiyo ƙararrakin harbin bindigu da tashin bomabomai da tsakar rana inda nan-da-nan aka samu ɗaukin gaggawa daga jami’an tsaron rundunoni.

Haka kuma, an ruwaito cewa matseretan sun karɓe akalar gudanar da gidan yarin inda suka yi ta nausawa ta ƙofofi masu rigunan kariya da buɗaɗɗun wayoyin tsaro da kuma ramukan ɓoya.

Sannan, a baya an samu lokuta mabanbanta har sau biyu da ƴan ta’adda ke ƙoƙarin kai hari gidan yarin waɗanda ake daƙile su.

Ministan harkokin cikin gida na ƙasar, a wata hira ta gidan rediyo, ya aika saƙo ga gwamnoni bayan tabbatar da aukuwar lamarin inda ya yi kira ga sarakunan ƙauyuka da malaman addinai da su kai ƙarar duk wanda ba a yarda da shi ba.

By Babaji