Tsadar rayuwa: Ina guje mana fushin talakawa – Sanata Lawan ya gargaɗi gwamnati

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja


Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya gargaɗi gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar ƙarancin abinci da kuma ƙarin kuɗin wutar lantarki domin kaucewa zanga-zangar talakawa da ka iya jefa ƙasar cikin ruɗani.
Gargaɗin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da al’amura ke ƙara taɓarɓarewa a Kenya, inda zanga-zangar adawa da matakin da gwamnati ta ɗauka na ƙara haraji ta rikiɗe zuwa neman ingantaccen shugabanci da kuma rajin cewa Shugaba William Ruto ya yi murabus.
Sanata Lawan (APC/Yobe ta Arewa) ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar na ranar Talata, yayin da ya ke bayar da gudunmawa ga ƙudirin da Sanata Karimi Sunday Steɓe (Kogi ta Yamma) ya gabatar tare da Sanata Mohammed Ali Ndume (Borno ta Kudu) kan “buƙatar gaggawar a magance matsalar ƙarancin abinci da kuma hauhawar farashin kayan masarufi a Nijeriya.”
Ya bayyana matsananciyar yunwar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta tare da jaddada wajabcin majalisar dattawa ta gaggauta shigar da ɓangaren zartarwa kan lamarin.
Lawan ya ce, “Idan ba mu ɗauki matakin gaggawa kan ƙarin farashin abinci da kuɗin wutar lantarki ba, ba za mu ji daɗi ba irin abinda za mu gani a kan tituna ba. Ba za ta yiwu mu ɗau wannan lokacin muna wulaƙanta al’umma ba.”
Ya kuma lura cewa rumbunan ƙasar nan babu komai a ciki kuma shigo da kayan abinci ya zama matsala saboda tashin darajar kuɗaɗen ƙasar waje.

By ukarofi