An buƙaci gwamnan Kaduna ya cire kwamitin riƙon ƙwarya a Birnin-Gwari

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wata ƙungiya mai suna ‘Birnin-Gwari Vanguard for Security and Good Governance’ da ke jihar Kaduna ta yi kira ga gwamnatin jihar da sauran masu-ruwa-da-tsaki da a rushe kwamitin riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Birnin-Gwari tare da ɗora zaɓaɓɓen ɗan takara.

Ƙungiyar ta yi hakan ne bayan da kotun ƙoli ta yanke hukuncin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi inda ta ce naɗa kwamitin riƙon ƙwarya da gwamnatin Kaduna ta yi a Birnin-Gwari ya ci karo da sakin layi na 7 a kundin shekarar 1999 na dokar ƙasa kamar yadda kotun ƙoli ta tabbatar.

Wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun shugaban ƙungiyar, Ibrahim Abubakar Nagwari ta ce yana da muhimmanci jama’a su sani cewa, an gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli a duka ƙananan hukumomi 23 na jihar, a ranar 23 ga watan Oktoba, 2021 wanda Hon. Yushau Ibrahim Aboki tare da wasu kansiloli ƴan jam’iyya ɗaya suka yi nasara inda kansiloli huɗu ƙaɗai aka bai wa takardar shaidar shiga ofishinsu.

A madadin bai wa Hon. Aboki takardar shaidar, sai gwamnatin jihar ta ƙaƙaba kwamitin riƙon ƙwarya a Birnin-Gwari tare da wasu kansiloli bakwai domin gudanar da shugabancin ƙaramar hukumar har zuwa yanzu.

Sannan, kotu ta aika da takardar umarni ga hukumar zaɓe ta jihar (SIECOM) da ta bai wa wanda ya yi nasara takardar shaidan fara aiki a ranar 12 ga watan Janairun 2022 wanda ba ta yi hakan ba. Daga nan, aka samu sanarwar fuskantar hukunci ga saɓawa umarnin kotun wacce ta fito daga ofishin Antoni Janar a ranar 10/11/2022, inda ta ce duk wanda aka samu da hannu cikin laifin, to za a kai mutum gidan yari.

Ƙungiyar ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mai bashi shawara kan harkar tsaro da Majalisar ƙasa da Darakta Janar na SSS da Sufeta Janar na ‘Yan sanda da Majalisar Dokokin jihar da Antoni Janar na jihar da kwamishinan ‘Yan sanda da su sanya baki a bai wa zaɓaɓɓun shugabannin karamar hukumar shaidarsu na fara aiki bisa la’akari da hukuncin kotun ƙoli na ranar 11 ga watan Yuli, 2024 tare da gaggauta rantsar da su gami da rushe tsarin riƙon ƙwarya a ƙaramar hukumar.

Kazalika, ta yi kira ga ƴan siyasa da manyan gari da al’umma baki ɗaya da su kiyaye dokokin tsarin mulki wajen ganin an samu shugabanci mai kyau, inganta tsaro da wanzar da zaman lafiya da kuma cigaba a ƙaramar hukumar.

By Babaji