An shiga juyayi yayin da ruftawar ginin makaranta ya kashe mutum 22 da raunata 120

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da wasu da dama daga cikin ƴan Nijeriya sun jajenta wa waɗanda ruftawar ginin makaranta ya rutsa da su a Jos wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka 22 da kuma raunata wasu 120.

Jaridar ‘Intel Region’, ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a yayinda ɗalibai suka shige ajijuwa a safiyar ranar Juma’a a makarantar Saint Academy da ke Busa Buji a jihar Filato.

Aƙalla, lamarin ya shafi ɗalibai 200 cikin na gidaje 400 na makarantar sakandaren waɗanda galibin su ƴan shekaru 15 ne ko ƙasa da haka.

A lokacin da yake magana kan lamarin, shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga ahalin da abin ya shafa da ma gwamnatin jihar inda ya ce ibtila’in babban rashi ne ga Nijeriya.

Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale a wani jawabi da ya fitar a daren Juma’a, ya ce shugaba Tinubu ya yaba wa hukumomin bada agajin gaggawa na NEMA da SEMA da ma ɗaiɗaikun mutane da suka kai ɗauki a yayin aukuwar lamarin tare da tabbatar wa jama’ar jihar samun taimakonsa a lokacin ƙuncin.

Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Caleb Murfwang ta tabbatar da aukuwar lamarin ta offishin kwamishinan yaɗa labarai, Musa Ashoms inda ta miƙa ta’aziyyarta ga ahalin waɗanda lamarin ya shafa tare da wakilta wata tawaga domin ayyukan kula da harkokin ibtila’in.

Sannan, gwamnan ya bada umarni ga dukkan asibitocin da aka kai waɗanda suka raunata da su basu kulawa ba tare da la’akari da batun biyan kuɗi ba.

Kazalika, ƴan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun PDP da LP na 2023, Atiku Abubakar da takwaransa Peter Obi sun jajenta tare da aika sakonnin ta’aziyyarsu ga ahalin mamatan ta kafofi daban-daban.

By Babaji