Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Wasu rahotanni da suka mamaye kafafen watsa labarai a ‘yan makwannin da suka gabata, na nuni da wani abu mai tsoratarwa na faruwa a gidajen aurenmu, kuma akwai haɗarin gaske idan aka bari ya cigaba ba tare da an ɗauki matakin da ya dace wajen kawo ƙarshensa ba. Kodayake ba sabon abu ba ne, amma yawaitarsa a wannan lokaci na bayyana cewa, jama’a sun fara kai wa maƙura.
Daga farkon wannan shekara kaɗai an samu rahotanni daban-daban dake bayyana yadda wasu matan aure suka yi sanadiyyar hallaka mazajensu na aure sakamakon dalilai mabambanta, wanda suka shafi saɓani kan zamantakewar aure. Saɓanin da za a iya warware su cikin lumana, ba tare da an kai ga zubar da jini ko asarar rai ba.
A ranar 13 ga watan Fabrairu, jaridar Leadership ta rawaito cewa wata amarya mai suna Aisha Aliyu daga Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja, rahotanni sun ce ta kashe mijinta Idris Ahmadu da wuƙa cikin tsakar dare bayan wani saɓani da suka samu, wanda aka ce yana da nasaba da auren dole.
A ranar 13 ga watan Mayu, jaridar Daily Post ta buga labarin wata mata mai shekaru 29 da ake kira Torkwase Kpile wacce amarya ce da basu jima da aure ba ita da mijinta mai suna Igbah Kpile dake ƙauyen Achusa a Ƙaramar Hukumar Makurɗi ta Jihar Binuwai ta cakawa mijin wuƙa a wuya har ya mutu, a dalilin ƙorafin yana takura mata da yawan saduwa.
Jaridar Ɓanguard ta ranar 3 ga watan Yuni ta buga rahoton wata mata mai suna Omolara Oluwakemi da ke ƙauyen Akungba na yankin Ƙaramar Hukumar Kudancin Akoko ta Yamma na Jihar Ondo, a dalilin zargin cin amanar aure da take yi masa. Rahoton ya ce, Omolara ta bugawa mijin nata taɓarya ne cikin dare yana barci.
Haka ita ma Zainab Isa mai shekaru 22 dake garin Damaturu na Jihar Yobe, jaridar Daily Trust ta ranar 26 ga watan Yuni, ta rawaito cewa, ta kashe mijinta Ibrahim Yahaya, sakamakon ƙorafin yana tauye mata haƙƙi ta hanyar hanata kuɗin cefane da zargin cin zarafi ta hanyar duka.
Jaridar Blueprint Manhaja ta ranar 5 ga watan Yuli ta buga wani rahoto ya bayyana yadda wata mata mai suna Maryam ta kashe mijinta mai suna Patrick John da fatanya a ƙauyen Faram-Faram dake Ƙaramar Hukumar Fufore a Jihar Adamawa a sakamakon saɓanin da suka samu akan wani ƙaramin siket da matar ke yawan sanyawa, wanda shi kuma mijin ya nuna ba ya so. Rahoton ya cigaba da cewa, matsalar ta afku ne da daddare lokacin da mijin matar ya dawo gida daga mashaya, sai ya haɗu da matar wacce ke ɗauke da juna biyu tana sanye da wani ƙaramin siket, wanda a baya ya gargaɗe da ta daina sakawa. An ce matar ta ɗauko fatanya ne ta buga wa mijin nata a goshi, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa bayan an kai shi asibiti.
Waɗannan rahotanni ba su kenan ba, don ko a cikin shekarar da ta gabata akwai rahotanni da dama da ke nuna yadda wasu mata suka hallaka mazajensu, ko dai ta hanyar makami ko kuma ta sanya guba. Kamar yadda Maimuna Suleiman mai shekaru 21 dake garin Bauchi ta daɓawa mijinta Aliyu Muhammad wuƙa har ya mutu a cikin watan Yuli na 2023, saboda dalilai na ƙiyayya.
Jaridar Daily Trust ta ranar 25 ga watan Nuwamba na shekarar 2023 ta fitar da wani sakamakon bincike da ta gudanar game da ƙalubalen cin zarafi a zamantakewar aure wanda a mafi yawan lokaci yake haifar da rasa rai. Binciken ya gano cewa akasari dalilan dake kawo waɗannan matsaloli na da nasaba da matsalar tattalin arziki da talauci, zargin cin amana, da rashin fahimtar juna ko fitar ƙauna a tsakanin ma’aurata.
Kamar yadda aka ji labarin yadda wata mata Fatima Abubakar a Jihar Ondo da ta kashe mijinta Goni Abba ta hanyar sa masa guba a abinci, saboda ta tsane shi, ba ta son zaman aure da shi.
A shekarar 2023 an lura da yadda ake yawan samun rahotannin kisan kai a tsakanin ma’aurata har ya ninka na shekarar 2022. Ga shi kuma a wannan shekarar ma adadin na so ya zarta na baya, idan har waɗannan kashe-kashe suka cigaba da aukuwa. Wani bincike ya gano cewa, maza sun fi cin zarafin mata ta hanyar duka ko cin zarafi, amma mata sun fi amfani da makami kamar wuƙa ko bindiga ko guba, suna kashe mazajensu. Kuma an fi samun irin waɗannan kashe-kashe a ƙauyuka ba cikin birane ba, inda ake ganin mutane na da sana’o’i da ayyukan da suka ɗauke musu hankali. Wata cibiya a ƙasar Amurka ta gano cewa, tun bayan annobar COƁID-19 rikice-rikice tsakanin ma’aurata sun ƙara tsananta a ƙasashen duniya, musamman a Turai, sakamakon ƙunci da takurar da jama’a suka shiga.
Mu ma a nan Nijeriya, idan muka lura da rahotannin da suke fitowa daga kafafen watsa labarai, da lokacin da abubuwan suke faruwa, za mu fahimci cewa tun bayan cire tallafin man fetur da aka shiga cikin tsananin rayuwa da lalacewar tattalin arziki, an samu ƙaruwar rabuwar aure musamman a jihohin Arewa, yawan saɓani tsakanin ma’aurata, da ƙaruwar cin zarafi da kisa a inda rikicin ya fi muni.
Duk da waɗannan rahotanni, har yanzu adadin da suka bayyana a hannun hukumomi da ‘yan jarida game da yadda ma’aurata ke kashe junansu, har yanzu maza ne ke kan gaba wajen muzgunawa mata, sannan mata ke biye. Amma abin tambaya me ya sa a yanzu matan suka fi ɗaukar makami suna halaka mazajensu, ba tare da shayin ko me zai biyo baya ba? A bayyane yake kafin namiji ya ɗauki wuƙa ko taɓarya, ko wani makami ya laftawa matarsa saboda wani saɓani ko ƙiyayya, yana da wahala, saɓanin yadda mata suke saurin hawa dokin zuciya, su biye mata kan duk abin da ta raya musu.
A mafi akasarin wuraren da irin haka ta faru, ana saurin bai wa matar da ta aikatawa mijinta kisan gilla wata kariya, inda za a ce ai ta yi haka ne don kare kanta, ko kuma a ce tura ce ta kai bango. Ko ma a ce mijin ne ya takura mata da jima’i, ita kuma ta ga ba za ta iya jurewa ba, sai ta kashe shi. Kamar misalin rahoton da muka kawo muku na Jihar Binuwai, da wanda ya faru wani lokaci a baya, a garin Jos, inda aka ce wata amarya ta yi wa mijinta yankan rago, don yana damunta da yawan kwanciyar aure. Shin kenan masu bai wa mata irin wannan kariyar suna nufin idan miji ya takurawa matarsa, tana iya amfani da makami ta kashe shi ba damuwa, duk cikin kare kai ne?
