Rundunar ‘Yan Sanda ta kama jami’inta kan zargin yi wa yarinya fyaɗe

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Rundunar ‘Yan sanda ta kama wani jami’inta mai muƙamin mataimakin sufuritanda kan zargin yin fyaɗe wa wata ƴar shekara 17 a Legas.

Ana zargin ɗan sandan mai suna Owolabi da samun damar afkawa yarinyar a ofishinsa da ke reshen rundunar a Ojota.

An kama shi ne bayan da hukumar yaƙi da cin zarafi ta jihar ta shigar da wata takarda ofishin kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Adegoke Fayoade wanda hakan ya sa kwamishinan ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da kama jami’in nasu inda ya ce a yanzu haka ana gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.

A lokacin da take magana kan lamarin, mahaifiyar yarinyar, Aramide Olupona ta zargi ‘Yan sandan da ƙoƙarin rufa-rufa wa al’amarin inda ta ce ta ga ƴarta tana zubar da jini ne bayan kwana ɗaya da faruwar lamarin, sobada haka sai ta kai ta wani asibiti wanda a nan ne aka tabbatar da kawar da budurcin nata.

By Babaji