Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta tabbatar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin halastaccen Sarkin Kano, inda kotun ta tabbatar da halascin sabuwar Dokar Masarautar Kano, wacce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaɓa wa hannu.
A yayin da ta ke yanke hukuncin, Alƙali Amina Aliyu ta kuma bayyana cewa, gazawar jami’an tsaro wajen tabbatar da an aiwatar da sabuwar dokar, shi ma saɓa wa dokokin ƙasa ne.
Haka nan ta kuma yanke hukuncin cewa, waɗanda ake ƙara ba su da hurumin hana Majalisar Dokokin Jihar Kano kafa doka a jihar.
