Tattaunawa tsakanin Tinubu da Ƙungiyar Ƙwadago akan mafi ƙaranci albashi za ta cigaba Alhamis

Spread the love

A ranar Alhamis 18 ga Yuli, 2024 ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shugabannin ƙungiyar kwadago za su sake haɗuwa domin ci gaba da tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, ya ce an kuma tattauna batun sabon mafi karancin albashin ma’aikata yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Litinin.

Idris ya ce shugaban ƙasar zai gana da shugabannin Ƙwadagon “domin kammala duk wani tattaunawa, sannan kuma zai sanar da ‘yan Nijeriya matakin da ya ɗauka ta hanyar aikewa ga majalisar dokokin ƙasar”.

Ana sa ran shugaban zai yanke shawara kan ƙudirin ƙwadago na ₦250,000 da kuma ƙudirin gwamnati na ₦62000.

A yanzu dai mafi ƙarancin albashin a Nijeriya shine ₦30,000.

By ukarofi