Gareth Southgate mai horar da Ingila ya sauka daga muƙamin sa bayan rashin nasara a gasar kofin Turai.
Wannan na zuwa ne, bayan shafe shekara takwas yana horar da ƙasar Ingila. Kocin mai shekara 53 ya buga wasanni 102, ya samu nasara a 61, sai kuma rashin nasara a wasanni 17. Shine kocin Ingila na farko da ya fara kai su wasan Ƙarshe har karo biyu.
Southgate ya fara riƙe muƙamin Kocin Ingila ne a matsayin mai riƙon ƙwarya a shekarar 2016 bayan saukar Sam Allardyce.
