Kotu ta ƙi amincewa da roƙon Emifiele na tafiya ƙasar waje don duba lafiyarsa

Spread the love

Mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotu da ke zamanta a Abuja, ya ƙi amincewa da ɓukatar tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emifiele, inda ya nemi koto ta bashi dama ya fita ƙasar waje domin duba lafiyarsa.

Mai sharia Muazu, ya shaida cewa Emifiele ya gaza kawo isassun abubuwa da suke nuna cewa tafiyar ta zama ta dole.

Mai shari’a ya ƙara da cewa, Emifiele ya ce asibiti ne suka gayyace shi, amma ya gaza kawo takardar gayyatar. Kuma ya gaza nuna cewa rashin lafiyan nashi, ba abin da ba za a iya dubawa a wannan ƙasar ba.

By ukarofi