
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Mai Shari’a James Omotosho na babban kotun tarayya a Abuja ya dawo da Philip Shuaibu a matsayin mataimakin gwamnan jihar Edo bayan Majalisar Dokoki ta tsige shi watannin da suka gabata.
Mai Shari’a Omotosho ya ce cire Philip daga muƙaminsa da majalisar ta yi bai halatta ba kuma ya saɓa wa dokar ƙasa.
Mai Shari’ar ya umarci da a biya Philip albashi da alawus ɗinsa tun daga watan Afrilu wanda a lokacin aka tsige shi.
Sai dai majalisar dokokin ta ƙi amincewa da hukuncin kotun inda ta shirya takardar ɗaukaka ƙara domin sake yin hukunci game da batun.
Ana ganin musabbabin abin da ya haddasa rikici tsakanin Philip da gwamnan jihar, Godwin Obaseki, akwai bincike da majalisar ta yi inda ta gano cewa yana bayyana sirrin gwamantin.
Saboda haka ne, majalisar ta naɗa kwamitin mutane bakwai domin yin hukunci kan lamarin wanda suka buƙaci a sauke shi inda cikin mambobi 19 da su ka halarci zaman tattaunawar, 18 sun buƙaci a tsige shi.
