Babbar kotu dake zamanta a Legas tayi watsi da ƙarar da aka shigar gabanta, a kan rubutun Larabci dake jikin kuɗin Naira.
Mai shari’a Yellin Bogoro yayi hakane yana mai dogara da sashe na 53 na dokar bankuna da sauran al’amuran kuɗi wanda ke cewa har sai an tabbatar an yi wani abu da wata manufa sannan kotu zata amshi wannan ƙorafin.
Kotun ta ƙara da cewa, ƙarar wanda wani lauya mazauni Legas ya shigar Malcom Omirhabo, yana mai ƙalubalantar rubutun Larabcin dake jikin takardar Naira ya gaza nuna wata shaida da ke tabbatar da cewa babban bankin ƙasa yayi haka ne da wata manufa marar kyau.
Amma a yau talata, kotu tayi watsi da wannan ƙara domin gaza kawo shaidu masu gamsarwa akan abinda ake zargin.
Sai dai Lauyan da ya shigar da ƙarar yace zasu amshi takardar hukuncin, sannan suyi tunanin mataki na gaba da zasu ɗauka.
A wani ɓangare kuma ƙungiyar MURIC tayi murna da wannan hukunci, tana mai cewa wannan ya nuna tabbas sashen shari’a na Nijeriya yana aiki.
