Za mu amshe duk wasu kujerun shugabanci, inji gwamnonin PDP

Spread the love

Ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, ta sha alwashin ƙwato dukkan muƙaman shugabancin da wasu jam’iyyun siyasa suka mamaye. Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ne ya yi wannan alƙawarin a wajen buɗe taron da aka yi ranar Laraba a gidan gwamnatin Jihar Enugu.

Gwamna Bala Muhammad ya cigaba da cewa “A yau mun zo ne domin haɗa kawunan mu, sannan mu tattauna batutuwan da suka shafi jam’iyya da al’amura daban daban da suka shafe mu”

Lokaci ya yi da jam’iyyar za ta ƙwato muƙamai na shugabanci a dukkan jihohin da a halin yanzu wasu jam’iyyu ke mamaye da su,” inji shi. Gwaman ya cigaba da cewa, ya yabawa Gwamna Peter Mbah bisa karbar baƙuncin taron da kuma kula da su tun lokacin da suka iso ranar Talata.

Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Sheyin Makinde na Oyo, Umo Eno na Akwa-Ibom, Sheriff Oborevwori na Delta, Bala Mohammed na Bauchi, Godwin Obaseki na Edo, Caleb Mutfwang na Plateau, Agbu Kefas na Taraba da Dauda Lawal na jihar Zamfara. Sauran sun haɗa da Ahmed Fintiri na Adamawa, da Douye Diri na Bayelsa ciki har da Peter Mbah na jihar Enugu wanda shine mai masaukin baƙi.

By ukarofi