Tinubu ya naɗa Esther Walson-Jack a matsayin sabuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin Mrs. Didi Esther Walson-Jack, OON, a matsayin Shugabar ma’aikatan Tarayyar Najeriya, inda zata karɓi ragamar aiki daga ranar 14 ga watan Agusta, 2024
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai baiwa Shugaban ƙasa shawara a kan harkar yaɗa labarai, Ajuri Ngelale a fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce sabuwar shugabar zata karɓi ragamar aikinr daga hannun shugabar ma’aikata mai ci a yanzu, Dr Folashade Yemi-Esan, CFR, wacce zata yi ritaya a ranar 13 ga watan Agusta, 2024.
Yayin da yake miƙa godiyarsa ga Shugabar ma’aikata mai barin gado a kan jajircewarta, shugaba Tinubu ya ƙalubalanci sabuwar shugabar ma’aikatan a kan gudanar da aikinta ta hanyar ƙirƙiro sabbin dabaru, riƙon amana, da kuma aiki a bisa kiyaye dokokin aikin gwamnatin Tarayyar Najeriya

By ukarofi