
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattijai ta yi kwaskwarima kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2024 ta hanyar ƙara tiriliyan N6.2 kan na shekarar da ta gabata.
Jawabin hakan na ƙunshe a cikin wata takarda da Tinubu ya aika wa shugaban majalisar, Goodwill Akpabio wacce aka bayyana ta a zaman majalisar na ranar Laraba.
Tinubu ya buƙaci hakan ne la’akari da samun goyon bayan sakin layi na 58 wanda reshe ne na sakin layi na biyu na kudin dokar ƙasa kwaskwarimar 1999 inda ya nemi majalisar ta amince da ƙudirin.
Ƙundirin gyaran dokar ta 2024, zai taimaka wajen bada damar samar da tiriliyan N3.2 ga ayyukan buƙatun rayuwa ga al’ummar Nijeriya baki ɗaya.
Sannan Naira tiriliyan 3 zai taimaka wajen fitar da isassun kuɗaɗen da ake buƙatar a kashe su wajen ayyuka da kuma daidaita lamuran kashe kuɗaɗen gwamnati.
Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa, ɓukatar kwaskwarimar zata taimaka wajen wajabta wa bankuna biyan kuɗaɗen haraji na ribar cinikin kuɗaɗen ƙasashen waje da aka samu a shekarar 2023.
Kazalika, ya ce matakin zai haɓaka ayyukan cigaba, ilimi, kiwon lafiya da sauransu a ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta al’amura da dama a Nijeriya.
