Hauhawar farashi: Majalisar Wakilai ta yi barazanar kama shugabannin simintin Dangote

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Wakilai kan ƙarin farashin siminti, a ranar Talata, ya yi barazanar damƙe mahukuntan kamfanin simintin Dangote idan suka gaza bayyana a zamanta na gaba.

Idan za a iya tunawa, a ranar 7 ga watan Mayun 2024 ne majalisar ta bada wa’adin kwanaki 14 ga masu kamfanin siminti da su gurfana a gaban kwamitinta na haɗin gwiwa tare da gabatar da ra’ayoyinsu kan ƙarin farashin siminti a Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba.

Shugaban kwamitin majalisar mai kula da ma’adanai, Jonathan Gbefwi ne ya yi wannan sammacin a wajen wani taron jin ra’ayin jama’a domin gudanar da bincike kan ƙaruwar farashin siminti a Nijeriya da kamfanonin samar da siminti suka yi, wanda kwamitocin haɗin gwiwar kasuwanci, masana’antu da ayyuka na musamman suka shirya a majalisar da ke Abuja.

A zaman da aka yi a ranar Talata, jami’an kamfanin simintin ba su halarci taron ba; lamarin dai bai yi wa kwamitin daɗi ba.

Kwamitin na musamman a lokacin da yake bayar da shawarar sake duba farashin siminti, ya nuna damuwarsa kan yadda farashin kayayyakin yake hauhawa a Nijeriya, ganin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

Ta umarci ƙungiyar masu kamfanonin siminti ta Nijeriya da babban bankin Nijeriya da su bayyana a gabanta nan da makonni biyu domin tattaunawa kan matakan da suka dace don magance lamarin domin amfanin jama’a.

A wani taƙaitaccen jawabi da ya yi a wajen taron, Gbefwi mai wakiltar mazaɓar Karu/Keffi/Kokona ta Jihar Nasarawa a dandalin jam’iyyar SDP, ya zargi masu kafanonin siminti da wahalar da talakawa, suna murmushi a bankuna ba tare da tausayawa ba.

“Su na son cin riba fiye da ƙima ba tare da jin tausayin ‘yan ƙasar da suka ba su wannan damar ba.

“A kan Dangote, hukuncina mai sauƙi ne. Dokokin sun ba mu ikon da ake buƙata amma muna bin ku sannu a hankali. Za mu ba ku dama guda ɗaya. Za mu yi magana da kwanan wata.

“Rashin bin wannan ranar, za a ba da sammaci. Za a ba ku sammacin kama ku don gabatar da ku a gaban Majalisar Tarayya. Babu wani mutum ɗaya da ya kai majalisar ƙasarsa girma. Babu wani ɗan Nijeriya da ya kai majalisar ƙasa girma,” Jonathan ya yi gargaɗi.

By ukarofi