Tinubu ya sauke surukin Buhari da wasu shugabannin hukumar buga kuɗi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta tsige Shugaban Hukumar Buga Kuɗaɗe da Muhimman Tarardun Sirri ta Nijeriya, NSPM, Alhaji Ahmed Halilu, tare da wasu manyan jami’ai huɗu.

Ahmed Halilu, ɗan uwa ga A’isha Buhari, uwargidan Buhari, wanda Buhari ya naɗa shi a cikin watan Satumba, 2022, yana daga cikin waɗanda Tinubu ya kora.

Sauran waɗanda korar ta shafa sun haɗa da Babban Darakta Ado Ɗanjuma, Babban Darakta na Legas, Chris Orewa, Babban Darakta Tunji Kazeem da Sakataren Kamfani, Ɓictoria Iraboh.

Ita dai Victoria Iraboh matar Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ce, wanda ya riƙe muƙamin Babban hafsan Tsaron Ƙasa a zamanin Buhari.

A yanzu na naɗa Babban Daraktan Ayyuka, Abubakar Minjibir matsayin Shugaban NSPM, sai dai ba a sani ba a san dalilin da ya sa shi ma Minjibir cin ba a cire shi ba.

Kokarin jin ta bakin Sidi Hakama kakakin babban bankin Nijeriya CBN ya ci tura. Sai dai wani babban jami’in babban bankin ya tabbatar da korar jami’an da abin ya shafa.

Wannan girgizar da aka yi wa kamfanin ta zo watanni bayan rahoton Jim Obazee mai binciken badaƙalar kuɗaɗe a CBN lokacin Godwin Emefiele, ya miƙa wa Shugaba Tinubu rahoton binciken da ya sa ya yi.

Rahoton dai ya bayyana irin mummunar rawar da Kamfanin Buga Kuɗaɗe a ƙarƙashin Ahmed Halilu surukin Buhari ya taka, a harƙallar buga sabbin kuɗaɗe, lamarin da ya kusa durƙusar da Nijeriya da ‘yan ƙasa bakiɗaya.

By ukarofi