Harin Gwoza wani zagon ƙasa ne da ake yi wa shirin gwamnatina na maida mutane matsugunnin su – Zulum

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya nuna cewa harin bom da aka kai a ƙaramar hukumar Gwoza, wani aiki ne na zagon ƙasa ga shirin sake maida ‘yan gudun hijira matsuganansu da gwamnatinsa ke yi.

Zulum ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a filin jirgin saman Muhammadu Buhari dake Maiduguri, bayan ya dawo daga hutun kwanaki 28 inda ya halarci aikin Hajjin shekarar 2024.

Zulum ya ce, “Abin da ya faru a Gwoza abin takaici ne matuƙa a wannan muhimmin lokaci da muke bikin ficewar ‘yan Boko Haram a jihar Borno, mun ga jerin hare-haren boma-bomai.”

Ya ƙara da cewa, “Na yi imani wannan wani aiki ne na zagon ƙasa, domin a wannan lokaci da muke sa ran ganin yadda za mu sake maida mutane zuwa yankunansu. Ina ganin wasu ba sa son ajandar sake maida su a jihar Borno.

Ya kuma ce, “Ina so in yi kira ga al’ummar Gwoza da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda. Gwamnatin jihar za ta haɗa gwiwa da gwamnatin tarayya don tabbatar da cewa an tsugunar da ‘yan gudun hijira a yankunansu.”

A halin da ake ciki Gwamna Babagana Umara Zulum ya jaddada ƙudirinsa na tallafawa manoma da magance matsalar ƙarancin abinci a jihar Borno.

Gwamnan ya ce “Za mu tabbatar da cewa mun yi fiye da abin da muka yi wa al’ummar jihar Borno. Na san akwai ƙalubale a Nijeriya, musamman matsalar ƙarancin abinci. Amma ina jin na wucin gadi ne.

Ya ƙara da cewa, “Gwamnati daga yanzu har zuwa ƙarshen gwamnatina za ta mayar da hankali wajen noma, faɗaɗa wuraren da ake nomawa da kuma tabbatar da ƙaruwar samar da abinci a jihar. Gwamnati za ta samar da iri ga manoma kuma za mu haɗa kai da gwamnatin tarayya don tabbatar da samar da abinci.”

Yayin da yake tsokaci kan aikin Hajji na shekarar 2024, Zulum ya ce, “A iya sanina, an samu ci gaba a ayyukan Hajjin bana idan aka kwatanta da shekarun baya. Ina ganin wannan yana ɗaya daga cikin mafi kyawun ayyukan Hajji a ‘yan kwanakin nan”.

Gwamna Zulum ya yaba wa gwamnatin tarayya da hukumar alhazai ta ƙasa bisa tabbatar da gudanar da ayyukan Hajji ba tare da cikas ba.

By ukarofi