Tunzurin ‘yan Nijeriya akan shirin zanga-zanga

Spread the love

 

Muhawara tsakanin malamai da matasa ta yi zafi, musamman a zaurukan sada zumunta da minbarori, inda kowanne ɓangare ke kare matsayarsa kan muhimmancin fita yin zanga-zangar lumana don yaƙi da matsin tattalin arziki, ko kuma barin fitar, saboda fargaba kan abubuwan da ka iya biyowa baya.

Kowanne a cikin waɗannan ɓangarori guda biyu na ganin matsayarsa ita ce ta fi dacewa a karɓa, don cigaba da zaman lafiyar ƙasar nan. Yayin da sauran ‘yan ƙasa suke a tsakiya suna kallon kowanne sashi da ganin girman matsayarsa. Kodayake wasu tuni sun ja layi, kowa na nuna ɓangaren da ya fi karkata.

In za mu iya tunawa daga ranar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta saba bayarwa ga manyan dillalan man fetur, a jawabinsa na kama mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 ‘yan Nijeriya suka shiga wani yanayi na ƙuncin rayuwa da rashin tabbas. A kullum rayuwa ƙara tsada take yi, yayin da yunwa da talauci suka addabi mafi akasarin jama’ar ƙasar nan. Duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnatin ta riƙa yi na samar da sassauci da tallafi a ɓangarori daban-daban. 

Duk da wannan hoɓɓasa da gwamnatin take nuna tana yi, rayuwa ta cigaba da yi wa ‘yan Nijeriya wahala, musamman ta fuskar abinci, sufuri, makamashin girki, kuɗin haya, kuɗin makaranta, da sauran buƙatun rayuwa na yau da kullum. Hatta mutanen da ake yi musu kallon su ne suke da dama-dama, halin da ake ciki su ma ya durƙusar da su. ‘Yan Nijeriya da dama ba sa iya samun abinci sau biyu a yini, ba ma a batun yin girki sau uku, wanda tuni ya daɗe da zama sai gidan wane da wane! 

Wannan ne ya fara janyo muhawara mai zafi a tsakanin ‘yan Nijeriya don neman mafita ga halin da ake ciki. Manazarta a kafafen watsa labarai har sun gaji da yin sharhi da ba da shawarwari ga hukumomi, suna ganin kamar ba a ɗaukar shawarar su, duk da ƙwarewar da suke da ita. 

Malam Isma’il Bello Usman da ke koyarwa a sashin Nazarin Tattalin Arziki a Jami’ar Jihar Bauchi, ƙwararre ne kan sharhi a kafafen watsa labarai game da abubuwan da suka shafi tattalin arziki, amma a cewarsa, lallai manazarta irinsa na jin gazawa da rashin ƙwarin gwiwa, saboda yadda suke ganin gwamnatin tarayya ba ta yin abin da ya kamata. Duk kuwa da ƙwararrun da suke tare da ita, yana ganin  hankalin gwamnati ya fi komawa kan tara kuɗaɗe ta hanyar haraji da tsare-tsare, a maimakon bunƙasa hanyoyin sarrafa tattalin arziki na cikin gida, wanda shi ne talakan Nijeriya ke amfana da shi kai tsaye. Ya ce, matakan da gwamnati take ɗauka na gyara tattalin arziki ita kawai yake amfana, ba ya isa ga talaka, shi ya sa yake daɗa fuskantar ƙalubale wajen kula da rayuwarsa da ta iyalinsa. 

Wannan dalili ne ya sa a kowacce rana a ƙasar nan kawunan jama’a ke daɗa ɗaukar ɗumi. Mu’amala da zamantakewa ke ƙara zafafa da taɓarɓarewa, yayin da ake samun ƙaruwar masu fama da cututtukan da suka shafi hawan jini da zuciya, har ma da lalurar taɓin hankali ko damuwar ƙwaƙwalwa, da yawan tunani suke yawa a tsakanin al’ummar ƙasar nan. A cewar likitoci da masana lafiyar ƙwaƙwalwa, sakamakon binciken ƙwararru. 

Dakta Maigari Yusuf Taru, ƙwararre ne a sashin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa a Babban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos ya bayyana cewa tun bayan da matsin tattalin arziki ya yawaita a ƙasar nan, mutane da dama sun shiga cikin wani yanayi musamman waɗanda ke da raunin ƙwaƙwalwa, ko waɗanda basa iya jurewa matsi da takura a rayuwarsu. Amma a nazarinsu na likitoci sun lura da ƙaruwar mutane masu zuwa da matsaloli masu nasaba da yawan damuwa ko yunƙurin kashe kansu, da masu shiga shaye-shayen sinadarai masu gusar da hankali, a watannin baya bayan nan. 

Yunƙurin da ya sake tasowa na buƙatar fita zanga-zangar ƙasa bakiɗaya daga wasu ƙungiyoyin fararen hula, na nuna yadda wannan matsin rayuwa yake damun jama’a. Yadda har wasu ke ganin tura ce ta fara kaiwa bango. An ga wasu saƙonni suna ta yawo a zaurukan sada zumunta da ke kira da ‘A kawo ƙarshen rashin shugabanci nagari!’ Kodayake babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin yaɗa waɗannan saƙonni da ke samun karɓuwa a wajen akasarin matasan ƙasar nan, musamman a nan Arewa. Sai dai kuma an ga wasu rubuce-rubuce da ke nuna goyon baya ga wannan yunƙurin fita zanga-zanga a shafin yanar gizo na tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar AAC (African Action Congress), Omoyele Sowore, wanda ke cewa, ‘babu abin da zai hana samun nasarar wannan tunzuri na neman kawo sauyi.’

Dama Sowore ba ɓoyayye ba ne wajen nuna adawarsa da halin da yanayin tsarin shugabancin ƙasar nan ke gudana. Muna sane da rawar da ya taka a lokacin zanga-zangar EndSars ta shekarar 2020, wanda ya haifar da ƙalubale mai yawa a fuskar tsaro da zamantakewar ‘yan Nijeriya. 

Ta iya yiwuwa wannan ne ya sa magabata da malamai a nan Arewa ke ƙoƙarin jan hankalin jama’a kada su ba da goyon baya a gudanar da wannan zanga-zanga ta ranar 1 ga watan Agusta, saboda abubuwan da ka iya biyowa baya, irin wancan na lokacin EndSars wanda aka yi zargin ɓata-gari sun shiga cikin masu zanga-zanga don haifar da ɓarna. 

Sakamakon haka har aka samu fashe-fashen dukiyar gwamnati da kayan jama’a har ma da asarar rayuka. Ina ganin don gudun sake aukuwar hakan ne ya sa malamai ke faɗakar da matasa illar da ke tattare da shiga wannan zanga-zangar da har yanzu ba a san masu shiryata ko tsarin da aka yi na gudanar da ita ba. 

Sai dai wannan ra’ayi na malaman ya gamu da fushin matasa waɗanda suka yi ta rubuce-rubuce na nuna rashin jin daɗin kalaman da malaman ke yi, a inda har wasu suka riƙa nuna rashin ladabi ga wasu malaman da suke gani zaƙewarsu ta yi yawa. Suna ganin idan har za a halalta yin zaɓe da siyasa to, bai kamata a hana yin zanga-zanga don nunawa shugabanni gazawarsu ba. Sabo Ibrahim Hassan na daga cikin matasa na gaba-gaba da ke ganin shiga zanga-zangar nan yana da amfani, domin farkar da shugabanni su yi abin da ya dace. Amma ba ya goyon bayan ra’ayin malamai da ke cewa kar a fita, a zauna a yi addu’a a nemi gafarar zunubai. 

A cewarsa, bai kamata malamai su yi shiru ko su kawar da kai daga halin da ƙasar nan ke ciki ba. Wannan shi ya sa ake ganin kamar da haɗin bakin wasu daga cikin su ga zaluncin da ke faruwa. Fitowar malamai ƙarara su ƙalubalanci masu shirin fita zanga-zanga yana ganin kuskure ne. 

Ya ce, ‘Ko dai malamai su yi shiru, ko kuma talakawa su zama abokan muƙabalarsu, don yunwa ba ta jin wa’azi balle ta gane nassi. Abin da yunwa ke fahimta kawai shi ne abinci.’ 

A yayin da nake ganin ba laifi ba ne don ‘yan ƙasa sun nuna wa shugabanni gazawarsu da buƙatar neman kawo gyara, kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin ƙasa, amma kuma lallai ne a lura da cewa ba a neman ‘yanci ko sauyi da rashin tsari ko rashin ladabi. Dole ya zama akwai jagoranci, akwai tsari, kuma akwai kiyaye doka. Lallai ne matasa mu lura da cewa yadda wasu ƙasashen suka cimma nasara wajen kawo gyara, ba lallai ne ya yi daidai da namu tsarin a nan ƙasar ba. 

Kada mu ruɗu da abubuwan da muke gani a kafafen sada zumunta, ko saboda ƙuruciya da zafin neman canji, mu bari wasu ɓata-gari da marasa kishin ƙasa su lalata mana manufar da muke da ita ta yin zanga-zanga cikin lumana. 

Kodayake da dama na ganin wannan zanga-zanga ba mai yiwuwa ba ce saboda rashin samun goyon bayan akasarin ’yan ƙasa, da matakan da jami’an tsaro suka ɗauka na daƙile yunƙurin masu neman tayar da zaune tsaye. Mu dai fatan mu shi ne gwamnati ta saurari kukan jama’ar ƙasa, waɗanda suka fita da waɗanda ba a jin muryoyinsu, don samar wa da talakan ƙasar nan sauƙi a rayuwarsa.

By ukarofi